Imrana Abdullahi
Ssnatan da ke wakiltar yankin kaduna ta tsakiya sanata Uba Sani ya bayyana cewa sun tattauna da wadansu wakilan kungiyar masu masana’antu da suka kai masu ziyara a ofishin shugaban majalisar Dattawa Alhaji Ahmed Lawan.
Sanata Uba Sani ya ci gaba da bayanin cewa sun dai tattauna a lokacin taron irin yadda za a hada hannu tsakanin majalisar da kungiyar masu masana’antu ta kasa domin a samu ci gaban da kowa ke bukata.
Za dai a iya cewa wannan yunkuri zai farantawa yan Nijeriya rai ganin irin yadda tsawon shekaru masana’antu a kasar suka durkushe ga kuma dimbin matasa maza da mata na gararambar neman aiki.