Home / News / Yan Takarar Majalisar Wakilai Sun Samu Nasara Ba Hamayya A Jihar Zamfara

Yan Takarar Majalisar Wakilai Sun Samu Nasara Ba Hamayya A Jihar Zamfara

Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga Jihar Zamfara na cewa yan takarar majalisar wakilai ta tarayya guda shida daga Jihar Zamfara sun samu nasarar tsayawa takarar ba tare da wata hamayya ba.
Sun dai tabbata da samun wannan nasarar ne a lokacin wani zaben fitar da Gwanin da ya gudana a Jihar.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Zamfara Yusuf Idris Gusau.
Wadanda suka samu nasarar sun hada da  Abba Ahmad Sani da zai wakilci kananan hukumomin Bakura/Maradun, Honarabul  Aminu Sani Jaji kananan hukumomin Kaura/Birnin Magaji sai  Isa Muhammad Anka kananan hukumomin  Mafara/Anka a majalisar wakilai ta kasa.
Sauran sun hada da  Honarabul  Sanusi Garba Rikiji Gusau/Tsafe, Alhaji Umaru S/Fada kananan hukumomin Shinkafi/Zurmi da  Alhaji Ahmad Usman Gummi kananan hukumomin Gummi/Bukkuyum.
Yayin da tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Maru/Bungudu, Honarabul Abdulmalik Zubairu Zannah Honarabul samu nasara a kan Alhaji Abdulrahaman Tumbido da Dr. Bashir Mohammed Maru inda ya samu nasarar tsayawa takarar.
Zaben fitar da yan takarar dai ya samu nasarar kammaluwa ne cikin yanayin kwanciyar hankali da natsuwa a gaban masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da kuma jami’an hukumar zabe ta kasa da jami’an jam’iyyar APC daga hedikwatar su ta kasa.
Reshen jam’iyyar na Jihar Zamfara ya yabawa yayan jam’iyyar bisa bin doka da oda da suka yi a lokacin zaben da kuma bayan zaben baki daya.
Shugaban jam’iyyar ya tabbatarwa da daukacin mambobinsa bayar da cikakkiyar dama ga kowa domin samun ribar Dimokuradiyya.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.