Home / Big News / Yawan Mutanen Da Suka Rasa Hanyar Cin Abincinsu A Kaduna Na Tayar Da Hankali – Isa Ashiru

Yawan Mutanen Da Suka Rasa Hanyar Cin Abincinsu A Kaduna Na Tayar Da Hankali – Isa Ashiru

Mustapha Imrana Abdullahi
….Ka Biya Ma’aikatan Da Ka Kora Hakkokinsu, Ashiru Ya Gayawa El- Rufa’I
Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019 da ya gabata Sarkin Bai na Zazzau Alhaji Isa Ashiru ya bayyana alhininsa tare da tausayawa wadanda suka rasa hanyoyin samun abincinsu sakamakon korar ma’aikatan da Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Nasiru Ahmad El- Rufa’i  ta yi wanda hakan ya kara Jefa dimbin jama’a cikin mawuyacin hali.
Alhaji Isa Ashiru ya ce kamata ya yi Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin Nasiru Ahmad El- Rufa’i ta dauki matsayin biyan ma’aikatan da ta kora a matsayin abin da ya fi komai muhimmanci, wanda hakan zai saukaka wa iyalai da dama su samu saukin rayuwa.
Ya dai bayyana hakan ne a cikin wata takardar da shi kansa ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a ranar Juma’a 9 ga watan Fabrairu 2021, a Kaduna, inda ya ce wadanda aka kora a halin yanzu sun shiga cikin mawuyacin hali.
“Samakon abin da ya faru, ina mika sakon jajantawa, albini da tausayawa wadanda wannan lamari ya faru da su tare da iyalansu, ina kuma son yin kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta shirya yadda za ta biya wadannan mutane Hakkinsu baki daya, saboda dukkan wani kokarin bata lokaci zai kara matsin tattalin arziki tare da kunci ne ga wadanda abin ya shafa”. Inji Sarkin Bai na Zazzau.
Ashiri ya ci gaba da cewa al’ummar Jihar Kaduna da dukkan yan Nijeriya baki daya su nan kuma su ma kallon irin abin da yake faruwa na korar ma’aikata da Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed El- Rufa’i ta aiwatar
” A yanzu dai kowa zai iya tabbatarwa cewa korar ma’aikata ya zamarwa wannan Gwamnatin wata manufa ce irin wadda suka kunso wa jama’a karkashin jam’iyyar APC tun da suka dare kan kujerar mulki saboda sun Sallami dimbin dubban ma’aikata daga matakin Jiha zuwa kananan hukumomi 23 tun a shekarar 2015 da suka kama mulki”. Inji shi
Ya bayar da misali da cewa idan aka hada alkalumman mutanen da aka kora aiki da kuma na wadanda suka rasa harkokin kasuwancinsu, za a iya ganewa cikin sauki cewa dukkan mutanen sun shiga wani kunci domin hanyar da suke samun abincinsu duk sun zama babu don haka hadari ne babba.
“Kamar yadda lamarin yake a halin yanzu, wadanda lamarin aikin Gwamnatin Jihar Kaduna ya shafa a dukkan fannonin rayuwa da suka hada da ma’aikatan Gwamnati,masu sana’o’in hannu da dukkan makarantan hakan, lamarin ya Jefa wasu cikin halin tsince taince a Bola
” Lamarin dai ya zamanto mai Jefa kowa cikin kaduwa kasancewar Gwamnatin APC ta kasa yin amfani da ingantaccen tsarin gudanar da aikin Gwamnati da ake da shi a Juhar Kaduna domin samawa jama’a sauki,sai kawai aka yi kokarin yin amfani da tsarin da zai haifar da matsaloli da ke girgunta al’amura baki daya”.
“Irin wannan halin, yanayi da tsarin da ake tafiya ya haifarwa ma’aikata,hukumomin Gwamnati da dukkan bangarorin da daukacin kananan hukumomi durkushewa sakamakon tashin karfin da suka shiga basa iya yin komai duk da muhimmancin da ya dace a duba a fadin Jiha”.
Kowa dai zai iya fahimtar cewa da wannan korar ma’aikatan ta kwanan nan da kuma wadda ta faru can baya, lallai alamace da ke nuni da cewa Gwamnatin da ke karkashin Malam Nasiru El-Rufa’i ba ta damu da halin matsin da jama’a suke ciki ba, wanda ya bayyana a fili cewa duk lamarin ya faru ne sakamakon irin manufar da suke da shi ta tafiyar da mulki.
” Dukkan wata Gwamnatin da ke da tunanin halin da mutane ke ciki za ta tabbatar ta duba tare da auna dukkan abin da za ta aiwatar kafin a yi shi, domin sanin irin yadda zai zama a rayuwar al’ummar kasa, musamman a wannan lokacin da ake fama da matsalar tsaro da tattalin arziki inda da dama suka shiga cikin talauci mai tsanani da ke cizon jama’a”.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.