Home / News / ZA A IYA SAMUN SABUWAR INGANTACCIYAR NAJERIYA – OLAWEPI HASHIM

ZA A IYA SAMUN SABUWAR INGANTACCIYAR NAJERIYA – OLAWEPI HASHIM

2023: OLAWEPO-HASHIM YA TSAYA TAKARAR SHUGABAN KASA
Bayan gudanar da tattaunawa da masu ruwa da tsaki daban daban a fadin Najeriya baki daya, matashi kuma sanannen dan siyasa da ke a kan gaba Mista Gbenga Olawepo – Hashim ya bayyana aniyar tsayawa takarar neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Olawepo-Hashim ya kammala shirin sayen fom dinsa domin tsayawa takara a ranar Alhamis mai zuwa a sakatariyar jam’iyyar APC da ke Abuja, ya jaddada cewa duk da irin halin da kasar take ciki game da batun yanayin tsaro, da kuma irin yadda tattalin arzikin kasa ke cikin wani mawuyacin hali sakamakon rashin matatun mai masu aiki da za su tace albarkatun man da ake da su  da kuma rashin wadatacciyar wutar lantarki da rashin samar da wutar da rarraba wa ga masu bukata, duk da hakan za a iya samun Sabuwa kuma ingantacciyar Najeriya”.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar  2019, ya bayyana cewa “yanayin da harkar siyasa ke ciki a kasa na cikin wani mawuyacin  halin, saboda al’amuran kabilanci da yadda wasu ke daukar al’amuran da zafi duk sun mamaye yanayin siyasar da har suke neman kai wa ga samun rikici, kuma hakan na kokarin dakile duk wani shirin samar da kasa dunkulalliya mai al’umma daya”.
Ya kara da cewa abu na uku, “kuma wadanda suka mamaye harkokin su ne ainihin masu ilimi da suke a cikin jam’iyyu da a koda yaushe suke kokarin samun biyan bukatun kansu musamman a tsawon shekaru Ashirin da hudu bayan an fita daga mulkin soja”.
Dan takarar ya ci gaba da bayanin cewa irin kokarin da wasu masu kishin kasa suka yi tun a jamhuriya ta farko ya taimakawa Najeriya ta zamo ta farko a tsakanin kasashen Asiya da Afrika ta fuskar ma’aunin tattalin arzikin kasa da za a bayar da misali da kasashen Malaysiya da Tailan duk tuni an mance da shi,” duk da haka har yanzu akwai yadda za a yi a gargadi da wannan tsarin tattalin arzikin da wasu suka lalata, da nufin samar da ginanniyar sabuwar Najeriya mai inganci.
Kamar yadda ya ce, “wannan samar da karfin zai taimaka wajen samar da hasken da zai shafe duhu a kasar mu. Don haka akwai wani babban abin dubawa ga duk mai kishin kasa da nufin magance dukkan wani tsarin da zai kawo wa kasa cikas.
“Na fito ne domin tabbatar da matsayi na game da zama shugaban tarayyar Najeriya a zaben shekarar 2023 mai zuwa”.
“Ni nawa ba wai buri ba ne kawai sai dai wani al’amari ne da ya kasance na tarihi da ke tare da ni tun a lokacin da ina karatu a jami’a mu na ta fafutuka kamar yadda kowa ya Sani, da a halin yanzu muke kokarin samar da bunkasasshen tattalin arziki a Najeriya, da kuma kokarin samar da ingantaccen tsarin mulkin Dimokuradiyya”.
Ya kara da cewa “babu wani abu da zai gagari yan Najeriya daga yanayi da kuma taimako. Saboda haka na fito ne in samar da shugabanci da zai samar da yanayi mai kyau a kasa”, ya kuma yi alkawarin cewa ya na da tsare – tsaren tattalin arzikin kasa da za su bunkasa Najeriya da za a samu sabuwar Najeriya da ya na samar a cikin Kudirori 50 za a fitar da su ga kowa ya gani nan ba da dadewa ba da ikon Allah”.
Hamshakin dan kasuwar na kasa da kasa mai sana’ar Man fetur ya ci gaba da tabbatar da cewa “sabuwar Najeriya da za ta iya zama da kanta a ciki da wajen kasar musamman daga duk wata barazana, da za ta samawa matasan ta aikin yi da a halin yanzu suke neman aiki za a samu ingantaccen tattalin arzikin kasa da nufin rage radadin talauci da cin hanci da karbar rashawa duk za a iya cimma wadannan bukatu domin masu yuwuwa ne”.
Ya yi alkawarin dinke barakar da take tsakanin Arewa da kudu a Najeriya, domin magance ciwon a dawo da kasar dunkulalliya da ake zaune tare da Juna kamar yadda aka Santa a can baya.
“Ni mahaifina ya kasance dan Arewacin Najeriya ne kuma mahaifiya ta yar Kudancin Najeriya ce. Don haka rabi daga cikin dangina Kiristici be wasu kuma Musulmai ne.
“Na zauna na yi makaranta a bangaren kudu da Arewa haka kuma a yankin tarayyar Turai da Amurka. Don haka na san cewa kowa an halicci dan Adam duk daya ne don haka suke da yanci dai- dai, samun dama da yi wa kowa adalci.
” Zan yi wa kowa adalci ba tare da nuna wani bambanci ba game da batun kabilanci, addini ko nuna mace ko Namiji. Wannan fa ba wani alkawari ba ne da ba zan iya cikawa ba kamar yadda wasu yan siyasa kan yi. Hakika ni haka nake”, inji shi.
Tun lokacin da yake kokarin ganin ya kare hakkin jama’a tsawon shekaru Talatin da suka gabata, Olawepo – Hashim ya yi abubuwa da dama a harkokin kasuwanci sabanin sauran wadansu da suka yi zamansu cikin jin dadi kamar yadda aka saba su na tafiyar da kungiyoyi masu zaman kansu, Kafafen yada labarai da kuma yin aiki a cikin jami’o’i.
A matsayinsa .a shugabannin farko a siyasa bayan da sojoji suka kau a shekarar 1999, ya zamo mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyya mai mulki da kuma shugaban gungun mutane 54 na majalisar zartaswar jam’iyyar da su kansa ya kafa.
Ya fita daga cikin jam’iyyar PDP a shekara 2006 bayan da aka samu ja- inja mai yawa a kan al’amuran da suka shafi harkokin Dimokuradiyyar cikin gida na jam’iyya.
Ya yi karatun aikin jarida a matakin digiri daga jami’ar Legas, da kuma karatun digiri na biyu a kan harkokin da suka shafi duniya a jami’ar Buckingham da ke kasar Ingila inda ya zamo dalibin da ya fi kowa kwazo a wannan lokacin abin da ya bashi damar zamowa na farko a cikin jerin daliban da suka yi karatu a wannan lokacin.
Olawepo-Hashim wanda ya kasance ya na cikin shekarunsa na Hansin, ya zama matashi mai jiki a Jika da ke da masaniya a game da harkokin tattalin arziki, harkokin tsaro da dukkan yadda za a inganta su lamarin da ya sha yin magana a kansu a tsawon shekaru hudu da suka gabata.
Ya ce yana da kwarewa sosai a aikace da kuma ta hanyar rubutu ban da kuma yadda yake yin harkar kasuwanci irin na kasa da kasa. Ya kuma yi karatu a harkokin kudi na kasa da kasa, harkokin tattalin arziki na kasa da kasa da kuma harkokin tsaro na kasa da kasa baki daya.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.