Home / News / BA ZAMU CI AMANAR KOWA BA – IBRAHIM DATTI YARON KIRKI

BA ZAMU CI AMANAR KOWA BA – IBRAHIM DATTI YARON KIRKI

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Dan takarar majalisar wakilai ta tarayya karkashin jam’iyyar NNPP Kwamanda Ibrahim Datti da ake yi wa lakabi da “kwamanda”, ya bayyana cewa babban abin da zai mayar da hankali a kansa idan an zabe shi dan  majalisar wakilai ta kasa shi ne rikon gaskiya da Amana.
Ibrahim Datti da wasu ke kiransa da Yaron kirki ya bayyana hakan ne a wajen taron murnar bikin Sallah da aka tara yayan jam’iyyar NNPP a  Jihar Kaduna.
Datti ya ci gaba da cewa ” idan an zabe shi zai tabbatar da rikon gaskiya da Amana a tsakanin al’umma saboda haka idan kuka ba ni amanrku ba zan yi kasa a Gwiwa ba”, inji Datti.
Matasa maza da mata sun halarci wannan taron inda suka yi jawabin bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga tafiyar Datti Kwamanda Yaron kirki, abin da suke bayyana da cewa tafiya ce ta neman tsira da mutunci martaba da samun natsuwa da ci gaban da kowa ke bukata.
Abba Umar Paki mazabar Ung Sanusi na daga cikin wadanda suka halarci babban taron walimar yayan jam’iyyar NNPP da Honarabul Ibrahim Datti yaron kirki ya kira da aka yi a Kaduna.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.