Home / Labarai / Za A Kammala Gyare gyaren Filin Wasan Ahmadu Na- Funtuwa

Za A Kammala Gyare gyaren Filin Wasan Ahmadu Na- Funtuwa

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI

Bayanan da muke samu daga Katsina na cewa an shirya kammala aikin ginin filin wasa na Ahmadu Na- Fintuwa da ke cikin birnin Katsina a farko watanni uku na wannan shekarar.

Bayanan dai sun tabbatar mana cewa an kasa aikin ne zuwa kashi biyu na farko shi ne yin kwaskwarima na rumfunan da ake amfani da su wajen kallon wasa da kuma wayar da aka zagaye filin wasan da ita,gyaran hanyoyin ruwa,samar da tankar ruwan da kuma samar da ingantacciyar ciyawa a filin wasan.

A ta bakin mai kula da ayyukan Abubakar Yusuf Sada,ya yabawa Gwamnati mai ci a yanzu karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari saboda irin muhimmancin da take ba harkokin wasanni domin bunkasa su.

Ya kara da cewa domin a yanzu harkar wasanni ita ce ainihin yaren da duniya ke amfani da shi wanda yake taimakawa matasa su kauracewa aikata miyagun ayyuka musamman ta fuskar shan miyagun kwayoyi da sauran miyagun al’amura.

Abubakar Yusuf Sada ya kuma tabbatar da cewa irin yadda kwamishinan kula da harkokin wasanni da matasa Alhaji Sani Aliyu Danlami ke aiwatar da ayyukansa a ma’aikatar a fili lamarin yake cewa za a samu ci gaba a bangaren wasanni.

Su kuma shugabannin kulab din wasa na Katsina Yunited kira suka yi ga magoya bayansu da su ci gaba da aiwatar da harkokinsu na nuna hadin kai da goyon baya domin samun gudanar da harka cikin ladabi da biyayya musamman a lokutan da ake gabatar da gasar wasanni.

Jami’in kula da harkokin yada labarai na kungiyar Malam Nasir Gide ya shaidawa manema labarai cewa magoya baya da ke nuna Soyayya ga kulab din ya zama wajibi su gujewa yin wani halin da zai Sanya a ci tara ko kuma a kakaba wa kulab din duk wani Takunkumi sanadiyyar faruwar wani abin da ba dai- dai ba.

 

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.