Home / Labarai / Za’ A Yi Amfani Da Matsalar Tsaro A Kori APC Daga Mulki – Masari

Za’ A Yi Amfani Da Matsalar Tsaro A Kori APC Daga Mulki – Masari

Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa kamar yadda aka yi amfani da matsalar tsaro aka Kori jam’iyyar PDP daga mulki in ba a yi hattara ba to haka za a yi amfani da matsalar tsaron a kori APC daga mulki.
Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin da ake kira da Masari Hadimin al’umma da ake yadawa a kafar yada labarai ta Talbijin ta Liberty.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen wani taro a Jihar katsina, inda ya bayyana cewa irin yadda wadanda ba su je makaranta ba kuma ba ilimin addini babu na Boko, amma kuma sun kware wajen harbin bindiga da kuma yi wa jami’an tsaro kenton bauna to lallai hakika akwai wata magana.
“Yayan APC da kuma daukacin jama’a akwai rawar da kowa zai taka wajen tabbatar da tsaron kasa da dukiyar jama’a
Ya kuma ce akwai asarar kwarai irin yadda ake rasa rayukan jami’an tsaro akwai asara babba saboda irin dukiyar da aka kashe kafin a samu jami’an tsaro manya da kananansu sai Gwamnati ta kashe kudi masu yawa kwarai.
Ya yi kira ga masu taimakawa yan ta adda da su guji yin hakan domin a karshe lamarin a kan mai yin hakan zai dawo.
“Mun dauki irin zagin da ake yi masu a matsayin shugabanni a matsayin Kaddara ta shugabanci”.
Mutane su yi addu’a da kyakkyawar niyya domin abubuwa suzo da sauki cikin nasarar da kowa ke bukata.

About andiya

Check Also

NASCON grows turnover by 37%, assures Shareholders of Continuous Growth, Value Creation

NASCON Allied Industries Plc has assured its shareholders of continuous growth and value creation in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.