Home / News / Saboda Zato Muka Goyi Bayan Buhari – Rufa’I Sani Hanga

Saboda Zato Muka Goyi Bayan Buhari – Rufa’I Sani Hanga

Sanata Rufa’I Sani Hanga tsohon shugaban Jam’iyyar CPC na tarayyar Nijeriya ya bayyana cewa zato ne kawai yasa suka shiga hidimar shugaba Muhammadu Buhari na tsawon shekaru da dama.
Rufa’I Sani Hanga ya bayyana cewa shi da kansa na narkar da dukiyarsa da suka hada da sayar da gidansa ya yi wa tafiyar Buhari hidimar siyasa  da kudin domin zaton da suke yi wa Buhari a can baya.
“Mu duk abin da muka yi wa Buhari duk mun yi shi ne a kan zaton Talakawa za su samu abin da ake zato na fita daga kangin da ake ciki tsawon lokaci a Nijeriya, amma bayan da Buhari ya dare karagar mulki sai muka ga duk ba haka bane”. Inji shi.
Hanga ya ci gaba da cewa ” Da wani mutum ya tambaye ni shin wai me yasa baka je ba ka karbi abin da aka nada ka, nan take na ce masa Bana so ne, sai ya ce amma kada ka ce komai ga don Allah. Wai an bani board member ne ka asibitin Oweri, ni kuma na ce Bana so shi yasa naki zuwa”.
Nan gaba kadan zamu kawo maku irin yadda ya sayar da gidansa da kadarorinka saboda yi wa siyasar Buhari hidima da yadda ya yi shekaru sama da Goma yana hidimtawa bangaren tafiyar Buhari da abin da ya biyo baya lokacin da aka kafa Gwamnati.

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.