Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ya kara jaddada kudirin ta na ganin fannin tattalin arziki da rayuwar jama’a ya ci gaba da bunkasa.
Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi wajen bikin ranar Jihar Katsina a kasuwar duniya ta kasa da kasa karo na 42 da aka yi a babban filin taro na kasuwar da ke kan titin Kaduna zuwa Zariya
Gwamnan wanda mataimakinsa Alhaji Munnir Yakubu ya wakilta wajen ranar Jihar Katsina ta wannan shekarar, inda ya ce babu wani abin da Gwamnatin Jihar ta Sanya a gaba irin ganin an samu ciyar da tattalin arziki da al’ummar Jihar gaba.
“Gwamnati na matukar kokarin ganin jama’a sun samu ingantacciyar rayuwa wanda hakan ya sa ake aiki a bangaren masana’antu,bunkasa kasuwanci da yin aiki tukuru domin ganin harkar tsaro ta inganta a duk fadin Jihar baki daya”.
Ya kuma ce Kofar Gwamnatin Jihar a bude take wajen yin maraba da baki masu son zuba jari a Jihar tun daga bangaren ciniki da masana’antu, harkokin yawon shakatawa, kullum ana kara inganta harkokin Noma da dukkan fannonin da za su ciyar da Jihar gaba.
A wannan kasuwar duniya ta kasa da kasa da ke ci a yanzu Jihar Katsina ce tsawon shekaru ba su yi fashin halartar wannan kasuwar ba, wanda hakan ne ya Sanya ta zamo Jiha ta farko a wannan shekarar 2021 karo na 42.
Domin daukacin kananan hukumomin Jihar baki daya da ma’aikatu, kamfanoni masu zaman kansu da yan kasuwa duk sun halarci kasuwar ta ba na.