Za Mu Fito Kamar Tururuwa A Gobe – Yan Kwadago
Mustapha Imrana Abdullahi
Yayan kungiyar Kwadago ta kasa a tarayyar Nijeriya sun bayyana cewa duk da irin abin da ya faru na kai wa yayan kungiyar tare da shugabanninsu na kasa hari a garin Kaduna za su fito kamar Tururuwa a Gobe domin ci gaba da abin da suke yi na kwatar yanci kamar yadda suke ce Gwamnatin Nasiru El- rufa’i na sallamar ma’aikata ba tare da bin ka’ida ba.
Yayan kungiyar ta kwadago sun shaidawa wakilinmu cewa duk da irin abin da ya faru da wadansu tsirarun yan Ta’adda suka kai masu hari lokacin da sansanin rundunar yan kwadagon ta kasa suka tsaya a shatalai talan da ke kusa da ofishin raba hasken wutar lantarki a titin Ahmadu Bello cikin garin Kaduna.
“Su dai wadannan batagarin sun iso wurin da muka yi sansani ne a shatalai talan cikin Kaduna kusa da ofishin hukumar rarraba wutar lantarki da ake kira KEDCO”, inji yayan kungiyar kwadago.
Yan kwadagon sun tabbatarwa da wakilinmu da ya dan tattauna da su cewa wannan kai masu harin da aka yi ya kara masu kwarin Gwiwar azamar fafutukar da suke yi na kwatar yancin da Gwamnatin Rl- Rufa’i ke kokarin tauye masu tun farko.
“Wannan dalilin na tauye hakkin jama’a da dama da suka hada da ma’aikata da masu sana’o’i da kuma yan Tireda da suke kasuwanci a wurare daban daban duk an rushe masu wuraren da suke neman abincinsu ba tare da yin la’akari da abin da ya dace a yi ba, kai wasu ma an rushe masu gidajen da suke zaune kowa ya san hakan, don haka na za mu daina wannan fafutukar kwatar yancin da muke yi ba sai mun cika wa’adin gargadi da muka ce za mu yi na kwanaki biyar, in kuma ba a daina abin da ake yi mana ba to lamarin fa zai yi girma kwarai”, inji yayan kungiyar kwadago.