Daga Imrana Abdullahi
Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna Jonathan Asake ya bayyana cewa sun kammala shiri tsaf domin kafa Gwamnatin da za ta rungumi kowa da kowa a Jihar Kaduna baki daya.
Jonathan Asake ya bayyana hakan ne a wajen babban taron kaddamar da yan kwamitin Yakin neman zabensa da kuma mataimakinsa Alhaji Bashir Aliyu Zangon Aya su dari hudu da Hamsin (450) da aka yi a babban dakin taron Sidi Resort da ke cikin garin Kaduna.
Dan takarar Gwamnan na Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar Lebo,Jonathan Asake,ya kumayi godiya ya fara yi ga dukkan jama’ar da suka samu halartar taron kaddamar da mambobin Yakin neman zaben jam’iyyar Lebo su Dari hudu da Hamsin (450)domin tabbatar da samun nasara.
Hakika ina farin cikin yadda dimbin jama’a suka halarci wannan taron kaddamar da masu Yakin neman zaben Asake da Bashir Aliyu
“Ina tabbatar maku cewa wannan Gwagwarmaya ce da ke bukatar kowa ya Sanya hannunsa domin alamu duk sun nuna cewa jama’a sun rungumi jam’iyyar Lebo, da nufin Najeriya ta zamo kasar da ke samar da dukkan kayayyakin da ake bukata, a samu ingantaccen tsarin da kowa zai yi murna da shi.
Muna yin kira ga dukkan yan jam’iyya su yi aikin neman zabe cikin kwanciyar hankali da lumana domin nasara ta mu ce, Peter Obi da Jonathan, Yan majalisar Dattawa sanata Bamalli, Auta da Muhammad Ibrahim duk tare da dukkan yan takara za su samu nasara baki daya.
Muna fatan Allah ya tabbatar mana da zaman lafiya, kwanciyar hankali tare da karuwar arziki a Najeriya baki daya.
An kuma kaddamar da kundin da ke dauke da irin kudirorin da za su aiwatar a Jihar guda biyar.
Taron ya samu halartar manyan jiga Jigan jam’iyyar a cikin da wajen Jihar da suka hada da sakataren jam’iyyar Lebo na kasa, Alhaji Audi, tsohon shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin Jihar Kaduna, yan takarar kujerun majalisun Jihohi, tarayya, Dattawa da sauran yayan jam’iyya an kuma yi taron lafiya an tashi lafiya.