Home / KUNGIYOYI / ZA MU KAWAR DA TALAUCI DA RASHIN AIKIN YI A NAJERIYA – ALIYU MOHAMMAD WAZIRI 

ZA MU KAWAR DA TALAUCI DA RASHIN AIKIN YI A NAJERIYA – ALIYU MOHAMMAD WAZIRI 

ZA MU KAWAR DA TALAUCI DA RASHIN AIKIN YI A NAJERIYA – ALIYU MOHAMMAD WAZIRI

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI

Honarabul Dokta Aliyu Muhammad Waziri, shugaban kungiyar masu fafutukar koyawa jama’a yadda ake neman zamani ta kasa ya bayyana gamsuwa da jin dadinsa bisa yadda aikin horas da masu koyon kiwon kaji yake tafiya a yankin Kano ta tsakiya cikin Jihar Kano a Arewacin tarayyar Najeriya.

Honarabul Aliyu Mohammad Waziri, da ake yi wa lakabi da   “Dan marayan Zaki”, ya ce dalilin zuwansa wannan wuri da ake aikin horas da jama’a masu koyon yadda ake kiwo da kulawa da  kaji shi ne saboda irin yadda yake samun labari na farin ciki da jin dadin yadda lamarin ke tafiya, “saboda haka ne na ce lallai sai nazo domin in ganewa idanuna yadda lamarin ke tafiya, kuma zuwan da na yi hakika na ga wannan farin ciki domin yadda ake gaya Mani hakan abin yake gudana”.

Hakika abin da na gani ya yi mini dadi sosai kuma na ga masu aikin horaswar da kuma daliban da suke koyon aikin duk abin na tafiya dai- dai, aikin likiticin dabbobin na tafiya kamar yadda ya dace”.

Dokta Waziri ya ci gaba da cewa daga kowace karamar hukuma akwai mutane Sittin da biya (65) da suke halartar taron horaswar, kuma za a yi wannan aikin a dukkan kananan hukumomin Jihar Kano a kananan hukumomi Arba’in da hudu (44) kuma dukkan wadanda suka halarci wannan taron za su ci gajiyar abin da aka tanada danga ne da kungiyar masu Noman zamani ta tanada.

Ya ci gaba da cewa babban dalilin yin wannan tsarin na horas da mutane shi ne domin a kawar da fatara da talauci.
” saboda ayi maganin irin abin da ke faruwa danga ne da dalibai masu kammala karatunsu amma su dinga yawo haka nan ba abin yi da wadansu mu da suke zuwa su na yin karatun a kasashen waje sun zo karatu amma su kare ba abin yi”, inji Dan marayan Zaki Dokta Aliyu Waziri.

“Kuma tsarin da muka dauko a halin yanzu zai taimaka a samu sahihin tsarin kara bunkasa ayyukan likitocin Dabbobi domin hakan zai kara taimakawa wajen inganta aikin da suke aiwatarwa, binciken da aka yi a halin yanzu daga cikin mutane kashi dari kashi sama da Sittin ba su san amfanin likitocin Dabbobi ba, amma yin wannan tsarin samun horaswar zai taimaka a samu biyan bukata har a Farfado da darajarsu da martabarsu jama’a su amfana da karatun da suka yi,kuma daga cikin tsarin mu akwai bukatar a samar da Likitan dabbobi a kalla mutum daya a kowace karamar hukuma wanda kuma yakasance dan karamar hukumar domin a fahimci mane ne Likitan Dabbobi kuma me zai iya bayarwa da nufin amfanar da al’umma.

A bisa dukkan alamu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu a wannan fannin, domin wadanda suka samu damar halartar taron horaswar sun bayyana gamsuwa da tsarin kamar yadda Fatima Muhammad da ta samu shiga cikin shirin daga karamar hukumar Beneji Jihar Kano da ta ce hakika ta karu sosai da wannan horaswar domin ta san yadda za ta kula da kaji yadda za a ba su abinci da Ruwan sha kai har ma da magungunan da za a ba duk wata kazar da ta kamu da rashin lafiya (sriya asabirina) ita ce cutar da ke kama kaji

Sai kuma Hafsat Shehu Idris, da ta ce sun koyi yadda sanin gane cututtukan da ke kama kaji har guda Bakwai zuwa Takwas, yadda zamu gane cewa kazar ta kamu da cuta kuma da yadda za a yi maganin abin.

Sai kuma Usman Muhammad Fage, ya ce hakika sun koyi abubuwa da yawa tun daga yadda za su yi kiwon kaji da kuma yadda ake kula da Kajin a koda yaushe, inda ya tabbatar da cewa sun koya kuma sun iya aikin don haka kwalliya ta biya kudin sabulu.

Kamar yadda wakilin mu ke bibiyar wannan aikin horaswar da kungiyar da ke kokarin Koyar da Noman zamani ke aiwatarwa ya nuna a fili cewa shirin zai taimakawa iyayen yara da kasa baki daya wajen kawar da damuwar da suke da ita ta fuskar rashin aikin yin da matasa ke fama da shi domin za su samu damar dogaro da kansu har wasu su samu cin gajiyarsu a koda yaushe.
Aliyu Waziri ya kara da cewa yanayin horaswar shi ne yadda jama’a za su san yadda ake kula da kaji tun daga dan sati daya zuwa sati Shidda yadda zai bayar da nauyin kilo biyu (2) kuma a san yadda za a kula da su kafin cutar ta zo an nemi maganin ta kuma a Koyar da su yadda za su bayar ko yin amfani da maganin.

Idan kuma abin ya fi karfin mutum sai ya bugawa likitan Dabbobi yadda lamarin yake, wannan ya sa a kowace karamar hukuma muka ware likitocin Dabbobi guda biyu domin su zama masu aikin horaswa ko a nan gaba.

Da suke jawabi ga manema labarai likitocin da suka bayar da horon sun bayar da tabbacin cewa wadanda suka horas hakika sun gane abubuwan da aka Koyar da su domin daga yadda suke amsa tambayoyi idan an yi masu kwalliya na biyan kudin sabulu kwarai.

Wasu daga cikin daliban sun ce abu na farko da ya dace su aiwatar shi ne a tsaftace dakin da za a ajiye kajin kafin a kawo su kuma da an kawo su za a ba kajin sinadarin gulukos su sha.

Dokta Kabiru Yakubu wani Likitan Dabbobi ne da ya fayyace yadda ya dace tun farko ayi inda ya ce za a tsaftace daki ko wurin da za a ajiye kajin, wato har in Sabo ne aji fashin magani tukuna a gyara shi in kuma Tsoho ne abin da za a yi na fin hakan yadda aka yi kwanaki biyu ko uku za kuma a ba kajin maganin gajiya wato bulkodi.

About andiya

Check Also

Northern Christian Leaders Pay Homage to Khalifah Sanusi, Strengthening Ties.

Northern Nigerian Christian Clerics Pay Homage to His Highness Khalifah Sanusi Lamido Sanusi to Strengthen …

Leave a Reply

Your email address will not be published.