Home / MUKALA / SULHU ALKAIRI NE – YUSUF DINGYADI

SULHU ALKAIRI NE – YUSUF DINGYADI

 

BOLA Tinubu da yaronsa na siyasa Rauf Aregbesola sun dai dai ta da juna, sun amince da yi wa juna uzuri saboda manufa ta ci gaban yankinsu bayan shugabanni da sarakuna na kabilar Yarbawa sun  shiga tsakani a asirce da baiyane.

 

Hakan na faruwa a dai-dai lokacin da mu a nan Arewa muke fuskantar rarrabuwa da rashin tabbas a kan makomar yankin mu da al’ummar mu; a fili bamu ga maciji da juna, sai yawan hassada, kiyayya da yarfe tare da neman cin mutunci da zarafin juna.

Yankin mu na Arewa yana cikin walagigi da kassarawa akan kowane tsari na rayuwa ga al’ummarsa tare da sakaci na shugabanin siyasa, Yan kasuwa, masu rike da madafun iko da sarauta har da malamai da yan boko da ma’aikata da sauransu sai cin duga-dugan juna don son kai, kwadayin da hassada muke yi.

Gyara ya faskara, ayi sulhu an kasa samun haka, talauci da rashin tsaro, lallacewa tattalin arziki da ilmi da harakokin rayuwa duk sai tabarbarewa suke yi a yankin mu fiye da sauran.

Shin yaushe Arewa zata hankalto don fita daga wannan mummunan yanayi na kassara juna da yiwa juna muguwar fata.

Allah ga AREWA!

Yusuf Dingyadi, Sokoto ne ya rubuto wannan mukalar.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.