Home / News / ZA MU TABBATAR DA TSARO,SAMAR DA AIKIN YI DA HADIN KAN KASA – PETER OBI

ZA MU TABBATAR DA TSARO,SAMAR DA AIKIN YI DA HADIN KAN KASA – PETER OBI

…ZA A SAMU SABUWAR NAJERIYA
DAGA IMRANA ABDULLAHI
Dan takarar shugaban kasa Mista Peter Obi, ya bayyana cewa kasancewar a matsayin Kaduna na hedikwatar arewacin Najetiya ne ya sa muka fara kaddamar da kamfe din mu a Kaduna.
Mu ba masu yin magana ne kawai ba saboda haka masu fada da cikawa ne, zamu tabbatar mun hada kan yan Najeriya baki daya.
Zamu tabbatar an samu ingantaccen tsaro a Najeriya ba zamu amince mutane su yi ta wahaka ba
“Samar da tsaro, aikin yi da kuma hadin kan kasa ne abin da zai tabbata a lokacin jagorancin mu”.
“Zamu mayar da Najeriya daga masu jiran yin amfani da kayan kasashen waje zuwa masu kirkira tare da samar da abubuwan amfani a daga masana’antun mu”.
A game da Kungiyoyin da suke taimaka mana to, ku dani hakika abin da kuke yi ba zai ta fi hakan nan ba kowa zai samu sakamakon alkairi na aikin da ya yi idan muka samu Gwamnati”.
Wannan lokacin da mutanen kirki ne za su zama suna cikin Gwamnati rike da madafun iko.
“Muna son mutane masu kwazo da sha’awar yin aiki wa kasa, na yi bikin murnar sabuwar shekara ne a sansanin yan Gudunhijira domin kada su ga kamar an manta da shi.
Idan kuka hada ni da Datti a wuri daga baki daya, za kufa cewa mu duk muna cikin shekarun mu ne na Hamsin, amma wancan ya na a Saba’in ne to, wancan fa?
Kasancewar yankin Arewa na Noma ya kasance wurin samar da abinci ga kasa don haka idan kun zabe mu Gwamnatin mu za ta inganta harkar Noma da samar da abinci a kasa.
Da yake nasa jawabin dan takarar mataimakin shugaban kasa Dokta Datti Baba Ahmad, cewa ya yi “ina masu shirin samun ilimi mai inganci, kiwon lafiya, tsaro, ina yi maku busharar cewa ga wani Bawan Allah na kawo maku domin takarar shugaban kasa, ab8n da ya burgeni da Peter Obi shi ne da ya ce daga Jihar Kaduna zai dauko don haka ina farin ciki da godiya kwarai”.
Ya ce “yana neman mutum mai ra’ayin a gyara kasa domin mu masu fadi da cikawa ne. Akwai masu ganin irin wannan taron suje suna takama, amma mu ni da Peter Obi zuciyar mu za ta sosu saboda ..
Ba zan kasance dannkasa mai rana kan jama’a ba domin ni mai kare gaskiya ne shi yasa nake tare da Peter Obi
Gwamnatin mu duk abin da ya samu mune duk abin da bai samu ba mune domin zamunyi wiki da gaskiya a koda yaushe.
“Shekaru 22 make fadin cewa talaka na da mutunci, Imani, lafiya da ilimi don haka duk zafin da kuke ji muna jin wannan zafin
Ga magana daya cewa da nake a majalisa an sayar da gidaje a Afo amma ni kadai ne ban says ba idan kuma akwai sheda to ya fito ya fade ta.
“Idan ba saboda jama’a da ci gaba nake yin wannan takara ba to Allah ya canza mani”
Da an ce Peter Obi ne shugaban kasa to mun Dakatar da kashe karshen da ake yi don haka muna kira gare ku ku ba  mu hadin kai ta hanyar kuri’unku kuma ba za su ta fi a banza ba, sabuwar Najeriya na tafe”.
Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar Lebo Mista Jonathan Asake ya yi kira ga daukacin al’umma da su tabbatar sun karbo tare da yin amfani da katin zaben su wajen zaben shugabannin da za su jagoranci kasar nan a zaben 2023 mai zuwa.
Jonathan Asake ya bayyana hakan ne a wajen taron gangamin da jam’iyyar Lebo ta shirya a Kaduna, domin yi wa dan takarar shugaban kasa Mista Peter Obi maraba da zuwa Jihar Kaduna, domin ganawa da mutane.
“Na yi maku alkawarin idan kun zabi jam’iyyar Lebo na zama Gwamnan Jihar Kaduna zan tabbatar da yi wa kowa adalcin da ya dace domin inganta rayuwar al’umma baki daya”

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.