Home / Labarai / Zamu Ajiye Matafiya Zuwa Kwana 14 – Gwamnatin Kaduna

Zamu Ajiye Matafiya Zuwa Kwana 14 – Gwamnatin Kaduna

Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar kaduna ta mika gargadi ga masu tafiya suna shiga domin su wuce ta Jihar kaduna cewa ko dai su kiyayi bi ta Jihar ko kuma a kama matafiya a ajiye su sai sun yi kwanaki 14 tsawon lokacin da ake killace masu cutar Korona bairus a tsare kafin a sake su.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta gargadi matafiya da ke kokarin karya dokar hana fita da su hanzarta kaucewa kudirin nasu ko kuma su gamu da tsarin killace mutane na tsawon kwanaki sha hudu.
 An cimma wannan matsaya ne a lokacin taron kwamitin da aka kafa domin yaki da kwayar cutar Covid – 19 kuma za a fara aiki da wannan mataki ne a gobe Alhamis 9 ha watan Afrilu, 2020.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun kwamishinan kula da harkar tsaro da al’amuran cikin gida Samuel Aruwan.
Gwamnatin ta bayyana cewa dukkan hanyoyin shigowa kaduna za a rufe su, kuma sai wadanda doka ta amince ne kawai za su samu kafar wucewa. Wadanda kuma ba a amince da su wuce ba za a ce masu su koma inda suka fito. Wasu kuma za a iya ajiye su a killace na tsawon kwanaki 14.
Dukkan wanda ba shi da wata takardar shedar da zai nuna, ana bashi shawara da su soke tafiyar da za ta kai su cikin Jihar kaduna. Domin an ba jami’an tsaro izinin su gaya wa mutane su koma inda suka fito a kan hanyoyin shiga misali hanyar Abuja zuwa Kaduna, Kaduna zuwa Birnin Gwari, hanyar Bwari – Jere – kangaroo, Gumel – Kwoi- Keffi sai hanayar Zariya zuwa Funtuwa da kuma hanyar Jos – Manchock.
Wannan hanin duknya shafi hanyoyin fita da shiga Jihar baki daya da ba a lissafi su a nan ba.
Gwamnatin Jihar kaduna ta Sanya dokar zama a gida ne domin kare lafiyar jama’a don haka ake tsaurara wa domin kiyaye mutane daga cutar Covid – 19 da ke gigita duniya a halin yanzu.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.