…Zamu yi Maganin Matsalar Tsaro
Daga Imrana Abdullahi
Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar PDP honarabul Isa Muhammad Ashiru Kudan, ya bayyana cewa sun shirya tsaf domin magance matsalar tsaro da kuma mayar da tallafin Takin Zamani domin samun bunkasa tattalin arzikin kasa baki daya.
Honarabul Isa Muhammad Ashiru Kudan ya bayyana hakan ne a cibiyar yan jaridu ta kasa reshen Jihar Kaduna lokacin da yaje domin ganawa da manema labarai inda ya bayyana wa duniya irin kudirorin da yake da su guda biyar wanda yake saran zai ba muhimmanci idan Allah ya tabbatar da nasarar lashe zaben Gwamnan Jihar Kaduna a shekarar 2023 mai zuwa.
Honarabul Isa Muhammad Ashiru ya ce ya tanadar da muhimman Kudirori guda biyar (5) da suka hada da tabbatar da magance
1 – Batun tsaro
2- Aikin Gona
3 – Yin ingantaccen gyara a kan harkokin ilimin kimiyya da fasahar kere – Kerr
4 – Lafiya
5 – Inganta rayuwar Matasa Maza da Mata.
Isa Ashiru ya kuma shaidawa manema labaran cewa zai tabbatar da samar da hanyoyi da kuma kwararru daga fadin duniya wajen cin moriyar ma’adinan da Jihar Kaduna keda su a shimfide a karkashin kasa, “saboda a Jihar Kaduna akwai ma’adanin da ake da shi wanda duniya ke nema domin ana sarrafa shi ta hanyoyi daban daban”.
Takarar na Gwamnan Jihar Kaduna a jam’iyyar PDP ya yi bayanai sosai a kan yadda zai taimakawa Jihar a samu warware batun bashin da ake ganin ya yi wa Jihar Kaduna katutu.
Musamman a Jihar Kaduna jama’a ba su bacci da idanunsu a rufe sai kullum a bude garau sakamakon matsalar rashin tsaron da ake fuskanta a ko’ina a Jihar, don haka da min zo Gwamnati ita ce farkon warwarewa”.
“Zamu mayar wa da masu rike da makaman sarautun gargajiya a wurare daban daban domin su ci gaba da aikin da suke yi shekarun baya na kula da harkokin tsaron dukiya da lafiyar jama’a”.
Matsalar talauci, hakika miliyan dari 133 suna cikin matsanancin matsalar talauci kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana saboda haka za mu tabbatar da yin wani abu muhimmi da nufin fitar da jama’a daga cikin wannan matsalar.
Sallamar ma’aikata ma ya taimaka kwarai wajen kara matsalar talauci kwarai, domin an Sallami ma’aikata aiki ba a ba su kudin su ba, to yaya ake son jama’a su yi da rayuwarsu.
A game da batun aikin Gona nan ma za mu tabbatar mun yi abin da ya dace wajen mayar da tallafin Takin zamani da kuma bayar da Takin ga manoma.
Ba kamar yadda lamarin yake a halin yanzu ba ga Takin zamani na tsada kuma amfanin Gona na arha, manomi a halin yanzu sai ya sayar da buhun Masara biyu idan ya na bukatar sayen Takin zamani, da wannan ta yaya za a samu ci gaban harkar Noma?
Ta yaya za a mayar da hukumar aikin Gona ta zama kasuwar sayar da kayan tireda?
“A duk duniya baki daya aikin Gona ne mai bayar da aikin yi ga jama’a mafi girma da yawa a duk duniya baki daya”.
Ta yaya za a inganta batun ilimin kimiyya da fasaha, wannan shi ne hanyoyin ciyar da al’umma gaba don haka mun Sanya wannan a gaba har sai hakarmu ta cimma ruwa.
A can baya muna da makarantun Koyar da sana’o’i (BATC) guda 23 a Jihar Kaduna, saboda haka muka yanke shawarar idan Allah ya bamu Gwamnati zamu gina guda daya a kowace karamar hukuma, ta yadda jama’a musamman ma matsa maza da mata za su dogara da kansu.
“Idan aka ba mu damar zama Gwamnan Jihar Kaduna zamu tabbatar mun samar da makarantun horar da jama’a ilimin sana’o’i guda daya a kowace mazabar dan majalisar Dattawa”
“Tallafin ilimi ya zama dole domin ba zamu iya bari a samu matsalar yan Ta’adda a kowane wuri ba”
Likita daya ya duba marasa lafiya dari 600, kamar yadda yake kunshe a majalisar dinkin duniya,amma a yanzu lamuran sun zama a cikin wani hali, don haka zamu samar da kayan aiki da likitocin da za su samar da komai.
” A Jihar Kaduna akwai Likitocin da ba su kai dari biyu ba, a Jihar da ke da yawan mutane ku san miliyan Goma yaya Likitocin za su yi da marasa lafiyar da ke halartar asibitocin Jihar”.
Kuma idan muka samu dama zamu samar da cibiyoyin kula da matsalar cutar Daji musamman ta Nonon Mata a yankunan dan majalisar Dattawa uku na Jihar nan domin taimakawa al’ummar jiha da kasa baki daya.
Muna tattaunawa da wasu wurare da dama a kan yadda za a taimakawa rayuwar matasa musamman matsan da suka kammala karatunsu amma ba aikin yi.
Ilimin sana’a za mu fi mayar da hankali a kai domin idan ka bar mutum ba aikin yi to, wasu fa za su iya samawa kansu aikin yi ta kowace hanya.
Dan takara Isa Muhammad Ashiru, ya samu halartar cibiyar yan jaridun ne tare da babbar tawaga karkashin jagorancin babban Darakta janar da kwamitin Yakin neman zaben shugaban kasa da Gwamnan Jihar Kaduna Dokta Haruna Yunusa Sa’id Kajuru,dan takarar mataimakin Gwamnan Mista Markus Mamman,mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna,Malam Shu’aibu Gimi,Ruben Buhari, Yakubu Lere, Malam Sa’idu da dai sauran jama’a da dama da suka yi wa dan takarar rakiya.