Home / News / ZAMU KAFA MAKARANTUN HADDAR ALKUR’ANI UKU A KATSINA – DIKKO RADDA

ZAMU KAFA MAKARANTUN HADDAR ALKUR’ANI UKU A KATSINA – DIKKO RADDA

DAGA IMRANA ABDULLAHI
ALHAJI Dokta Dikko Umar Radda ya bayyana cewa a cikin kudirorin da yake kokarin kawowa domin neman gyaran al’amura a Jihar Katsina zai kawo tsarin makarantun HADDAR Alkur’ani mai tsarki a Jihar Katsina.
Dokta Dikko Umar Radda wanda yakasance dan takarar Gwamna ne a halin yanzu a Jihar Katsina ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron da aka yi na yan asalin Jihar Katsina mazauna garin Kaduna da aka yi a garin Kaduna.
Dokta Radda ya ce za a yi ingantaccen tsari ne na kowace shiyya za a yi makarantu masu inganci guda Uku kowace shiyya ayi makaranta guda daya, da za a ingantata a samar mata da kwararrun malamai, litattafai da kuma kayan koyo da koyarwa irin na zamani.
Kuma Za a rika Koyar da ilimin Lissafi da turanci da yadda komai zai samu inganta a samu mahaddatan Kur’ani kuma masana ilimin zamani ta yadda al’umma za ta inganta sosai.
Za kuma a samar da tsarin da wadannan mahaddata Kur’ani za su ci gaba da karatun jami’a har sai sun yi digiri kamar yadda ake yi a duk duniya.
“Ta yaya za a ce wanda ya yi karatun Alkur’ani har ya haddace shi amma kuma a rika daukar shi kamar bai yi ilimi ba? ni a wuri na mutum ne wanda babu mai iliminsa a ko’ina za a laluba cikin duniya domin Kur’ani ya hada dukkan komai duk wani ilimi a nan za a same shi, saboda haka ina gaya maku cewa mahaddata Kur’ani na da kima da darajar da babu mai ita ko a wurin Allah madaukakin Sarki don haka suna da gurbi mai yawa a cikin Gwamnatin Jihar Katsina”.
Dokta Dikko Umar Radda ya kuma yi bayanin cewa “Zamu dauki alkalummansu mu ga yawansu da abin da za a yi masu da nufin rayuwarsu ta inganta”, inji shi.
Kuma a kauyuka za a yi wani tsarin koya wa makarantar Allo da na Alkur’ani, ilimin lissafi da Turanci domin a samu dai daitawa da zamani, ta yadda za su iya ci gaba da karatunsu a duk jami’ar da suke bukata.
Za kuma mu samar da wani ingantaccen tsarin taimakawa matasa domin bunkasa rayuwarsu ta fuskar kula da harkokin wasanni kasancewar wannan bangare ya zama wata siyasar da take hada kowa da kowa a wuri daya ta fuskar hadin kai a duniya.
Kuma tsari ne da ya zama ana samun abin duniya da shi da har akwai wanda ya yi wasan kwallon kafa a duniya kuma ya zama shugaban kasar Laberiya, akwai kuma wadanda ke amfanar rayuwar jama’a da dama ta hanyar gudanar da rayuwar duniya a halin yanzu.
A wajen wannan taron dai jama’a da dama sun samu halartar wurin taron musamman ma wasu daga cikin mazaunan Kaduna da suka kasance yan asalin Jihar Katsina.

About andiya

Check Also

Northern Christian Leaders Pay Homage to Khalifah Sanusi, Strengthening Ties.

Northern Nigerian Christian Clerics Pay Homage to His Highness Khalifah Sanusi Lamido Sanusi to Strengthen …

Leave a Reply

Your email address will not be published.