Home / News / ZAMU TABBATAR DA AN YI WA YANKIN FUNTUWA ADALCI – DANDUTSE

ZAMU TABBATAR DA AN YI WA YANKIN FUNTUWA ADALCI – DANDUTSE

Daga Imrana Abdullahi
Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Kananan hukumomin Funtuwa da Dandume, kuma dan takarar Sanatan yankin Funtuwa da ake kira karaduw, Alhaji Muntari Dandutse ya bayar da tabbacin cewa za su tabbatar an yi wa kowa adalci tun daga Jihar Katsina zuwa kasa baki daya.
Alhaji Muntari Dandutse ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai, jim kadan bayan kammala babban taron katsinawa da Daurawa da aka yi a garin Kaduna, inda aka gayyaci dan takarar Gwamnan Jihar Katsina Dokta Dikko Umar Radda domin ya yi wa jama’a jawabin irin kudirorin da yake da su zai aiwatar idan ya lashe zaben Gwamnan Jihar a shekarar 2023.
Honarabul Muktari Dandutse, ya ci gaba da bayanin cewa ya na kira ga daukacin al’ummar tsohuwar Funtuwa tun daga karamar hukumar Funtuwa da kuma yankin Funtuwa da Jihar Katsina baki daya da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jam’iyyar APC da dukkan yan takararta a kowane irin mataki domin za a tabbatar da yi wa kowa adalci idan an kafa Gwamnati.
“Tsarin raba dai dai ba tare da yi wa kowa kwange ba, shi ne babban Burin mu, don haka kowane gari da yanki su tabbatar sun zabi jam’iyyar APC a kowane irin mataki saboda kwalliya za ta ci gaba da biyan kudin sabulu”, inji Dandutse.
Honarabul Dandutse ya ci gaba da bayanin cewa ” ni ba na Shakka ko wani kokwanton aje kowace mazaba da nake wakilta domin a tantance irin ayyukan da na kawowa jama’a, kuma ni ba wanda zai ce maka ina boyewa jama’ar da suka zabe ni ko ba na komawa gida kai duk wannan ba su cikin halayena a matsayin dan majalisa domin wakilci aka aike ni in yi a majalisar kasa kuma ina kokarin wakiltar jama’a kamar yadda ya dace”.
Sai Dandutse, ya kara yin kira ga daukacin jama’a da su kara ba shi damar zama dan majalisar Dattawa ta kasa domin ci gaba da samar da romon Dimokuradiyya ninkin baninkin irin abin da jama’a ke ga ni a halin yanzu
Ya kuma jaddada wa jama’a musamman na yankin Funtuwa da karamar hukumar Funtuwa cewa ba sauran yi wa wasu nakasu bayan an yi zabe sai raba dai dai domin babbar magana ce kuma dole a tabbatar da aiwatar da ita a koda yaushe.
“Mu abin da muke son talakan Jihar Katsina ya fahimta a matsayinsa na mutumin kirki mai sanin yakamata wanda ya san yau da Gobe, ya auna da hankalinsa a game da batun yan takarar da ake yin zabubbuka da su da mu a yanzu da muka tsaya zabe kuma muna takarar Sanata, mu uku ke yin takarar nan kuma dukkan mu mun yi majalisar tarayya to sai a auna mu a gani, a cikin mizanin hankali shin me ka yi wa al’ummarka, mene ne mutuncinka da sanin yakamatarka kuma a duba ma shin wake zuwa mazabarsa talakawa su gansu ba da ka zabe shi ace ka yi zaben tumun Dare ba da ba zai yi maka amfani ba, sai kawai mutum ya zauna a Inuwa ya yi Allah ya Isa kawai. Saboda haka muke fadakar da jama’a cewa ya na da kyau ka yi zaben abin da zaka gani kuma ya kawo maka ci gaba da nasarorin da baka yi tsammani ba na inganta rayuwa duniya da lahira”. Inji Dandutse.
A game da batun yin nade naden mukamai bayan an ci zabe, amma a mance da Funtuwa duk da muhimmancinta, sai Muntari Dandutse ya ce ” to Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, wannan hakika magana ce mai matukar muhimmanci kwarai , Saboda tsakani da Allah sai fa an duba sosai da idanun basira a game da wannan al’amari domin yankin Funtuwa an bar shi a baya a kan abin da ya shafi nadin manya manyan mukamai na Gwamnatin tarayya da sauran manya manyan nade naden da suka shafi Gwamnati. Amma muna godiya ga Allah da ya azurta mu da Gwamna kuma a lokacin farko da muka fara yi”.
Kuma “Ai ba za a hana mutane yin koke ba, ko ni kaina ina goyon bayan mukami kowane iri ne yazo wannan yankin domin ci gaba ne kuma idan aka samu ci gaba in dai mukami ne zai haifar da ci gaban aikin yi, amma abin da muke yin kira a nan shi ne su kara bayar da kuri’a sosai mai tarin yawa domin za mu tsaya tsayin daka muga cewa an yi taba dai- dai na mukamai domin wakilci nagari”, inji Honarabul Dandutse.

About andiya

Check Also

Aliyu Sokoto tasks cabinet on transformation drive, ‘ be committed and sincere 

  By Suleiman Adamu, Sokoto SOKOTO state Governor Dr Ahmed Aliyu Sokoto has tasked members …

Leave a Reply

Your email address will not be published.