….Tawagar Gwamnan Zamfara Ta Sauka Abuja
DAGA IMRANA ABDULLAHI
GWAMNAN Jihar Zamfara Dokta Muhammad Bello Matawalle ya kara jadda kudirinsa na kare martaba da mutuncin al’ummar Jihar Zamfara a duk inda suke a fadin duniya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin mai bashi shawara a kan harkokin hulda da kasashen waje da abin da suka shafi kungiyoyi Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, a lokacin da ya ziyarci al’ummar Zamfara mazauna garin Karmu a cikin babban Birnin tarayyar Abuja a Najeriya.
Gwamna Matawalle ya ci gaba da cewa ba za mu yi sako- sako da kare martaba da mutuncin al’ummar Zamfarawa ba a ko’ina suke a cikin duniya, domin babban aikin da ya dace ga duk wata Gwamnati shi ne ta kare mutuncin al’ummarta don haka muna kan hakan a koda yaushe.
“Akwai muhimmanci kwarai ga dukkan mutane yan asalin Jihar Zanfara a ko’ina suke su tabbatar da zaman lafiya da bin dokar duk wurin da suka samu kansu a wurin kuma akwai muhimmanci kwarai yan Jihar Zamfara su koma gida a lokacin kada kuri’a domin zaben shugabannin da za su jagoranci al’ummarsu ta yadda za a samu shugabanci nagari.
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, Mai bayar da shawara ne ga Gwamnan Jihar Zamfara a kan harkokin hulda da kasashen waje da kungiyoyi ya bayyana garin Karmu da cewa, Karmu kusan in ce mahaifata ce domin mu muka kakkabe ta daga baragurbi har a yanzu kuka samu zama a cikinta.
Tun a zamanin Jamhuriya ta farko ba wanda ya yi yunkurin duba jama’a kamar wannan Gwamnan, wanda sanadiyyar hakan ne aka shirya aiwatar da wannan ziyarar.
” Gwamna ya bamu sakon cewa daga yau babu wani mutum dan asalin Jihar Zamfara da za a ci hakkinsa face sai Gwamnati ta tashi tsaye wajen nemo masa, yancinsa a ko’ina ya samu kashi a fadin duniya, don haka kada ku yi wasa musamman wajen bin doka da ka’ida ta wuraren da kuka samu kanku ta fuskar zamantakewar rayuwar duniya”, Inji Matawalle.
Karmu ce asalin mahaifar duk wani dan Zamfara da ke cikin garin Abuja, don haka Gwamna ne gatan ku a yau, lokacin a rika yin watsi da bukatun ku ya wuce.
“Ina sanar da ku cewa duk wanda ya cinye maka hakki sai an kwato maku hakkin ku ko a hannun waye kuma ko a ina yake a fadin duniyar nan”, Matawalle ya tabbatar da hakan.
“Ku bi doka, ku kama sana’a kada ku yi duk wani abin da bashi a kan doka da ka’ida”.
Gwamna ya ce akwai muhimmancin kowa ya koma Gida ya yi zabe ku zabi Gwamna Dokta Bello Muhammad,Sahabi Ya’u, Umar S Fada da kuma Usman Mahmuda Aliyu Shinkafi, Shatiman Shinkafi, domin wadannan mutane za su ciro maku kitse a wuta da nufin samun ci gaba mai inganci.
“Abin kunya ne ace a lokacin zabe PDP ta samu kuri’a Goma a akwatin Zabe a Jihar Zamfara don haka ku duba fa da idanun basira, irin yadda halin da mutanen mu da suke ciki a Auchi, inda wasu batagari suka dauki wani yaro ya na tuka Babur aka kwakule masa idanu, Yaron nan idanu don haka sai an bi masa hakkinsa daga wurin Gwamnatin Jihar Edo, a kokarin nemo masa hakkin ne ma a yanzu za mu ta fi kotu sai yancinsa ya fito, an hukunta duk wadanda suka yi masa wannan aika aikatar da ya rasa wani bangare na jikinsa saboda haka alamace da ke nuni da cewa an dauki saitin ingantaccen gyara mai inganci”.
Hakazalika masu kiran mu Malu, Aboki ko ace wa dan Arewa Akuya bisa hakan ma mun ta fi kotu domin a hana kiran yan Arewa da wannan suna na kaskanci ga al’ummar Hausawa da wasu a yankin Kudu maso Yamma suke jifan jama’a da shi.
“Ba wani Gwamnan da yazo domin duba lafiyar ku a fadakar da ku abin da ya dace, Gwamna ya ce a baku gurbin aiki na SSA na mutum biyu”.
“Ni na bayar da Filin makabartar da ake magana a nan karmu domin na samu a wancan lokacin makabartar yar karama ce kwarai babu wadataccen fili, ina tabbatar maku cewa wannan aikin makabartar za a yi shi da ikon Allah.
Hakika wannan shugaban kungiyar yan asalin Jihar Zamfara Abubakar da ya yi maganar neman taimakon makabarta ya yi dai- dai, kuma a Gobe zaku ji batun tallafin mu, da ikon Allah.
Muna godiya da kuka yi wa Gwamna karamci kuma idan lokaci ya yi ku tabbatar kun koma Gida domin zaben Gwamna, Sahabi Ya’u, Umar Sa Fada da Usman Mahmuda Aliyu Shinkafi domin kara ciyar da Jihar Zamfara gaba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Darakta Janar Nasiru Yusuf, da ake wa lakabi da Ofisa, ni a can baya ban san wani Gwamnan da ya taimaki matasa kamar Dokta Bello Matawallen Maradun don haka muna yi masa godiya.
Ina kira ga mutanen da ke zaune a Abuja cewa sanadiyyar irin maganganun da Dokta Suleiman yake yi hakika an samu saukin matsalar tsaro a Jihar Zamfara baki daya.
” A duk Jihar Zamfara baki daya babu wani mutum ko dan siyasa da ya koma karamar hukumarsa kamar Dokta Suleiman Shu’aibu Shinakfi ya yi wa jama’a taimakon da yawa, tallafin da ya bayar ya hada da Injin Nika,Atamfofi ga Mata,injunan Taliya,Gina masallatai,Kwamfutoci tare da kayayyakinta,Wayoyin hannu da sauran abubuwan alkairi da yawa
Sakamakon hakan Gwamnan Jihar Zamfara ya kara yin Godiya ga wannan bawan Allah tare da yi masa jinjina mai karfi.
Darakta Janar Nasiru Yusuf Ofisa, ni a can baya ban san wani Gwamnan da ya taimaki matasa kamar Dokta Bello Matawallen Maradun ba, don haka muna yi masa godiya.
Ina kira ga mutanen da ke zaune a Abuja cewa sanadiyyar irin maganganun da Dokta Suleiman yake yi hakika an samu saukin matsalar tsaro a Iihar Zamfara baki daya.
” A duk Jihar Zamfara baki daya babu wani mutum ko dan siyasa da ya koma karamar hukumarsa kamar Dokta Suleiman Shu’aibu Shinakfi ya yi na taimakon jama’a da yawa tallafin Injin Nika,Atamfofi ga mata,injunan Taliya,Gina masallatai,Kwamfutoci,Wayoyin hannu da sauran abubuwan alkairi da yawa
Sakamakon hakan Gwamnan Jihar Zamfara ya kara yin Godiya ga wannan bawan Allah
Tun da farko shugaban yan asalin Jihar Zamfara mazauna garin Abuja ya ce akwai shugabanni da yawa da suka zo domin tarbar wannan tawagar Gwamna da ya aiko a ganmu a kuma tattauna da mu aji halin da muke ciki, Alhaji Abubakar Sani Shinkafi ya jaddada kudinsu ta fuskar bayar da duk wani hadin kai da goyon baya ga Gwamnatin da Gwamna Matawalle ke yi wa jagoranci.
Shugaba Abubakar Shinkafi, ya kara da cewa “Dokta Suleiman ba bakon mu ba ne, domin irin Namijin kokarin da Dokta Suleiman ne ya sa muka rabu da kaya wato wani mutum da yake addabar mu a can baya”, inji Abubakar Shinkafi.
Al’ummar Jihar Zamfara mazauna Abuja sun yi kira ga Gwamnati da ta taimaka masu kamar yadda ake taimakon kowa daga wurin Gwamnatin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Bello Matawalle mai kishin jama’arsa.
An kuma bayyana wa tawagar Gwamnan shugabannin da ke shugabantar kananan hukumomin da suka fito daga Juhar Zamfara da suke zaune a babban birnin tarayyar Abuja da suka hada da,Aliyu Bature Shinkafi karamar hukumar Shinkafi, Shamsu Ahmad Dan Nahuce Bungudu karamar hukumar Bungudu , ina zaune a nan karmu unguwar Hausawa, Allah ya sa wannan kokarin da za mu yi shi ne zai kawo mana asalin zaman lafiya
Muna fatan za a dauki matasan mu aikin yi da kuma samun hanyoyin ci gabane
“A wasu lokuta ana samun wasu matsaloli na rashin hanyar tafiya zuwa wurare da kuma rashin samun sanin wasu muhimman mutane da za su taimaka masa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso Allah ya ba da iko da darajar amin”
“Makabartar karmu na samun barazana kwarai don haka muna neman taimakon ayi mana aikinta”, inji shugaban Abuja Abubakar.
“Muna sanar da wannan tawagar cewa hakika a lokacin zabe za mu kasa mu tsare mu kuma tabbatar da an samu sakamakon zaben da al’umma suka zaba”.
Kaura Balli Yusuf Dogon Kade, wakilin matasan al’ummar Jihar Zamfara a Karmu duk sun bayar da tabbacin taimakawa Gwamnati
Daga cikin wadanda suka samu halartar taron akwai Hassan Muhammad Maru, wakilin matasan Maru baki daya, Usman Abubakar shugaban Zurmi, Malam Sani Nasiru Durumi 2 da Garba Muhammad Kabusa da sauran jama’a da dama musamman zunzurutun matasa.