Home / News / ZAN MAGANCE MATSALAR TSARO A NAJERIYA – WIKE

ZAN MAGANCE MATSALAR TSARO A NAJERIYA – WIKE

….Ya Ba Yan Gudun hijira Tallafin Naira Miliyan Dari Biyu A Kaduna
MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Ribas Mista Nyeson Wike ya bayyana cewa babban kudirinsa in zama shugaban tarayyar Najeriya shi ne ya magance matsalar tsaron da ke addabar kasar a matakin farko.
Nyeson Wike ya bayyana hakan ne lokacin da yake yi wa masu zaben wanda zai tsayawa jam’iyyar PDP takarar  shugaban kasa da ake kira (deliget) su 74 daga Jihar Kaduna.
A wajen wani babban taron da aka yi domin karbar bakuncinsa tare da tawagarsa a dakin taron jam’iyyar da ke NDA Kaduna, Wike ya bayyana cewa zai fara ne da yin maganin matsalar tsaro idan yan Najeriya suka zabe shi ya zama shugaban kasa.
Nyeson Wike ya kuma shaida wa masu zaben dan takarar shugaban kasa  na PDP daga Jihar Kaduna su 74  cewa idan sun zabe shi a matsayin dan takarar kujerar shugabancin Najeriya karkashin PDP, to, kowa ya tabbatar cewa za a samu nasarar lashe zabe ba tare da wata tantama ba ko kadan.
“Ina kira ga masu zaben dan takarar kujerar shugaban kasa daga PDP da su tabbatar sun zabi wanda zai iya lashe zaben kasa baki daya domin a samu sauki a kasa baki daya”.
Kamar yadda jama’a suka Sani a can shekarun baya babu wani shugaba a yankin arewacin Najeriya da bashi da gida a Kaduna, domin wuri ne na zaman lafiya da lumana kuma jama’a da dama komai Dare su na tafiya zuwa Kaduna daga Abuja, kai ko ni kaina ina minista ina zuwa Kaduna ne ta hanyar yin amfani da mota domin ko’ina lafiya kalau amma yanzu fa? kowa ya san rashin tsaro ya yi yawa.
Nyeson Wike ya kuma yi kira ga masu zaben dan takarar daga Jihar Kaduna da su bashi kuri’a Sittin (60) daga cikin kuri’u 74 na masu zaben wanda zai tsayawa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a shekarar 2023 mai zuwa, koda yake za a yi zaben fitar da Gwanin ne a ranar 28 da 29 na watan Mayu mai zuwa don haka ku zabe ni saboda ni ne dan takarar da zai iya tsayawa har sai nasara ta samu a koda yaushe.
Wike ya kuma ce ” duk yayan PDP su hada kansu shi kuma ya yi alkawarin zai taimaka masu idan zabe ya zo, saboda yayan PDP a Jihar Kaduna sun yi rawar gani a zaben kananan hukumomin da aka yi a Jihar domin sun samu kananan hukumomi shida (6) saga cikin kujerun da Jihar keda su 23 don haka a hada kai domin hakan shi ne mafita”.
Da yake tofa albarkacin bakinsa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Ahmad Muhammad Makarfi ya bayyana irin jajircewar Nyeson Wike da cewa ta haifarwa da jam’iyyar PDP da kuma wadanda suka yi hakuri a cikin ta da nasarar da ake ciki a halin yanzu .
Sanata Makarfi ya kuma bayyanawa taron taimakon kudin da Nyeson Wike ya bayar domin tallafa wa yan gudun hijira da suke a Kaduna tallafin kudi naira miliyan dari biyu lakadan.
Makarfi ya kuma yi alkawarin yin amfani da kudin kamar yadda ya dace ga wadanda aka bayar da kudin dominsu.
Kuma Sanata Ahmad Muhammad Makardi ya ce ” duk wanda ya damu da kai hakika kaima ka damu da shi”
Hajiya Hauwa Kida, ta gabatar da jawabi a madadin mata cikin harshen Turanci inda ta bayyana Nagarta da irin ayyukan alkairin da Gwamna kuma dan takarar PDP yake yi da ta bayyana su da abin farin ciki.
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna Nuhu Bajoga ya bayyana halayen Gwamna Wike da cewa sai wanda ya matsa kusa da shi kawai zai tabbatar da nagartarsa, saboda haka ya ce Nyeson Wike ya cancanci samun kuri’u 60 daga Jihar Kaduna.
Tun da farko sai da jagoran tafiyar fafutukar neman zaben Nyeson Wike a matsayin mai neman a tsayar da shi dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP tsohon Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Hassan Dan kwambo, ya bayyana dalilan da suka Sanya dan takarar nasa ya cancanci a zabe shi ya tsayawa PDP takarar shugaban kasa.
Yayan jam’iyyar musamman masu kuri’ar zaben dan takara a ranar zabe  sun bayyana gamsuwa da jindadinsu da irin yadda Gwamna Nyeson Wike ke taimakawa jam’iyyar.
Wasu daga cikin jiga Jigan yayan jam’iyyar PDP da suke cikin tawagar Nyeson Wike sun hada da Sanata Yakubu Lado Dan Marke, Sanata Nazifi, honarabul Yakubu Barde ( no shaking) a matsayin kodinetan tafiyar Nyeson Wike a Jihar Kaduna da dai sauran kusoshin PDP da dama.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.