Home / KUNGIYOYI / AN YI TARON TATTAUNAWA KAN ZAMAN LAFIYA A KADUNA

AN YI TARON TATTAUNAWA KAN ZAMAN LAFIYA A KADUNA

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
A kokarin ganin an samu kyakkyawar dangantaka a tsakanin mabiya addinai daban daban, an gudanar da taron tattaunawa na shugabannin addinai a Kaduna da ke tarayyar Najeriya.
 Taron tattaunawar dai kungiyar “Action Aid” ce ta shirya shi tare da hadin Gwiwar “Global Peace Development, da tallafin asusun Global Community Engagement and Resilence ( GCERF).
Da yake bayani a wurin taron, darakta Esike Eburuke wanda ya samu wakilcin ko – idineta na Kaduna na kungiyar kokarin samar da ci gaban zaman lafiya na Kaduna Uwargida Chat Sunday ta ce matsalar tashin hankali tsakanin mabiya addinai daban daban na kara kaimi a Najeriya.
 Ya bayyana cewa matsalar da ake samu ta tsattsauran ra’ayi na kara kaimi a cikin al’umma daban daban musamman ta fuskokin al’adu, tsarin zaman yau da kullum da addini.
Inda ya kara da cewa cibiyoyin addinai da kuma al’umma su na kara samun matsalar tashe tashen hankula kwarai.
Ebruke, ya bayyana hakan ya haifar da matsalolin tashe tashen hankali na gaggawa da yawa da suka hada da samu matsalolin cikin gida da matsalar tsugunnar da mutane sakamakon rikici. Sai ya tabbatar da cewa wadannan kalubalen da ake samu sun haifar da tsarin kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya.
Da yake nasa jawabin Darakta Janar kula da harkokin addinai na Jihar Kaduna wanda ya samu wakilcin mai rikon Darakta a harkokin addinin Kirista, Uwargida Gora Catherine Safiya cewa ta yi samar da batun zaman lafiya na da matukar muhimmanci a kowa ce al’umma.
Saboda haka ya na da kyau ga daukacin jama’a su fahimci juna, domin haka ta hanyar samun tattaunawa ne mutane za su fahimci junan.
Saboda haka ne suke yin kira ga wadanda suka shirya wannan taron da su ci gaba da yin taro irin wannan a cikin al’umma ta yadda jama’a za su san muhimmancin zaman lafiya.
A nasa bangaren Ko- dinetan kungiyar Action Aid, Anicetus Atakpu cewa ya yi dalilin gudanar da wannan taron a Kaduna shi ne domin a samu karfafa dangantaka tsakanin dukkan bangarorin da nufin yin maganin matsalar samun tsattsauran ra’ayi tsakanin mabiya addinai da suka yi Imani.
Ya kuma yi bayanin cewa shugabannin addini na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen dakile matsalar tsattsauran ra’ayi da kuma maganin samun yawan tashe tashen hankula.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai wakilin kungiyar Jama’atunnasrul Islam na Jihar Kaduna Alhaji Ibrahim Kufena, wakilan kungiyoyin Matasa daga bangaren addinin Kirista da Musulmai sai kuma Sakataren kungiyar Kiristoci ta CAN reshen Jihar Kaduna, sai kuma mai gayya mai aiki uban tafiya Fasto Yohannah Y. D Buru da samu halartar taron tare da tawagarsa baki daya.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.