…Zamu yi aiki tare da kowa
…Za mu Gina Al’umma
DAGA IMRANA ABDULLAHI
Sabon zababben Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana cewa zai yi wa kowa adalci a lokacin tafiyar da jagorancin Jihar Kaduna da Allah ya bashi.
Sanata Uba Sani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a dakin taro na Yar’aduwa da ke harabar dandalin wasanni na Murtala a cikin garin Kaduna, jim kadan bayan karbar shaidar takardar lashe zabe (satifiket) daga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.
” zan yi wa kowa adalci da wadanda suka zabe mu da wadanda ke siyasa da kuma wadanda ma ba su siyasa har ma wadanda ba su zabe mu ba duk za mu yi masu adalci a wajen tafiyar da mulkin da za mu yi a Jihar Kaduna”.
“Za kuma mu gina jama’a domin kowa ya san irin halin da ake ciki a kasa.
Sanata Uba Sani Gwamnan Jihar Kaduna ya kuma godewa kowa, musamman wadanda tun ranar da aka kaddamar da kamfe ba su zauna ba har sai da aka samu nasara.