Home / News / ZAN YI WA KOWA ADALCI -GWAMNA UBA SANI

ZAN YI WA KOWA ADALCI -GWAMNA UBA SANI

…Zamu yi aiki tare da kowa

…Za mu Gina Al’umma

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Sabon zababben Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana cewa zai yi wa kowa adalci a lokacin tafiyar da jagorancin Jihar Kaduna da Allah ya bashi.

Sanata Uba Sani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a dakin taro na Yar’aduwa da ke harabar dandalin wasanni na Murtala a cikin garin  Kaduna, jim kadan bayan karbar shaidar takardar lashe zabe (satifiket) daga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.

” zan yi wa kowa adalci da wadanda suka zabe mu da wadanda ke siyasa da kuma wadanda ma ba su siyasa har ma wadanda ba su zabe mu ba duk za mu yi masu adalci a wajen tafiyar da mulkin da za mu yi a Jihar Kaduna”.

“Za kuma mu gina jama’a domin kowa ya san irin halin da ake ciki a kasa.

Sanata Uba Sani  Gwamnan Jihar Kaduna ya kuma godewa kowa, musamman wadanda tun ranar da aka kaddamar da kamfe ba su zauna ba har sai da aka samu nasara.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.