Home / News / 2023: Gwamna Matawalle Ya Yi Alkawarin Samawa Matasa Aikin Yi, Magance Rashin Tsaro

2023: Gwamna Matawalle Ya Yi Alkawarin Samawa Matasa Aikin Yi, Magance Rashin Tsaro

IMRANA ABDULLAHI
Gabanin zaben shekarar 2023 mai zuwa Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammaed Matawalle ya bayyana kudirinsa na yin maganin matsalar tsaro da kuma samawa matasa ayyukan yi a duk fadin Jihar.
Matawalle ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Jihar da su zabi APC, ya ci gaba da cewa zaben jam’iyyar APC zai taimaka wajen samar da tsaro da kuma ayyukan yi a Jihar.
Da yake jawabi a ranar Talata lokacin kaddamar da Yakin neman zaben shekarar 2023 domin sake neman a zabe shi a matsayin Gwamnan Jihar a wajen wani babban taron da aka yi a garin Kauran Namoda, inda ya tabbatar wa da jama’a cewa Jihar Zamfara a yanzu jiha ce ta jam’iyyar APC.
Tsofaffin Gwamnonin Jihar Alhaji Ahmad Sani Yarima da Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi duk sun yi jawabai sosai a kan bukatar da ake da ita na a samu ci gaban Gwamnatin Matawalle saboda a ci gaba da aiwatar da ayyukan da aka fara nan Gwamnatin Bello Mohammed Matawalle a kammala su a samu Dorawa daga inda aka tsaya.
Dukkan su sun yabawa Gwamna Matawalle bisa irin yadda yake kokari a tafiyar da Jihar.
Tsohon Gwamna Abdul’Aziz Yari Abubakar, wanda shi ne jagoran Yakin neman zaben Dawowar Gwamna Dokta Bello Matawalle a shekarar 2023 ya yi kiran a mika wuya baki daya wajen bayar da cikakken hadin kai da goyon baya domin sake zaben Matawalle a 2023 domin hakan zai taimaka wajen ci gaba da ayyukan da ake aiwatarwa a Jihar.
Ya bayyana hakan ne a lokacin farko inda ya ce dukkan jiga – Jigan siyasar Gwamnatin Jihar Zamfara duk sun hadu a wuri daya. Saboda haka ne ya shawarci jama’a da kada su zabi kowa ce jam’iyya sai APC tun daga sama har kasa kuma a koma lokacin shekarar 1999 inda dukkan Jagororin siyasar Jihar Zamfara ke magana da yawu daya sakamakon dunkulewar da suka yi ba tare da nuna bambanci ba ko kadan.
Gwamna Bello Matawalle, ya bayyana cikakkiyar gamsuwarsa tare da murna da irin yadda dimbin taron jama’a suka taru a wajen kaddamar da zaben shekarar 2023 ba za a ba jama’a kunya ba domin tsare tsaren samar da romon Dimokuradiyyar da ake samar wa a Jihar Zamfara za su karu ne wanda saboda haka ne ma Allah yake taimakon mu muke yin magana da aikin zamantakewar siyasa da yawu daya.
Samun hadin kai da aka yi daga dukkan bangarorin jiga Jigan siyasar Jihar da suka dunkule wuri daya alamace ta za a samu ci gaba a Jihar Zamfara.
Ya yi alkawarin samar da ayyukan ci gaba a ko’ina a duk fadin Jihar idan an zabi jam’iyyar APC al’ummar Jihar Zamfara za su more rayuwa.
Ya kuma yi bayanin cewa daukacin masu ruwa da tsaki,shugabannin jam’iyya,yan jam’iyya da masoyan jam’iyya da su hada kai su zabi APC da dukkan yan takarar ta saboda kamar yadda ya ce za a samar da tsaro da zaman lafiya da kuma samar da ribar Dimokuradiyya ga jama’a.
Yari, wanda ya kasance jagoran Yakin neman zaben shekarar 2023 domin sake zaben APC a karo na biyu ya jaddadawa mama’s cewar za a ci gaba da samun ci gaba a dukkan kananan hukumomi Goma sha hudu (14) na Jihar.
Ya kuma bayyana gamsuwa da irin yadda jama’a suka rungumi lamarin jam’iyyar APC musamman wajen ganin an samu nasara a zabe mai zuwa.
Sai ya kara da cewa Jihar Zamfara ta APC ce tun dadewa saboda haka muke kara fadakar da jama’a cewa kowa ya tabbatar nasara ta tabbata a zaben shekarar 2023.

About andiya

Check Also

Aliyu Sokoto tasks cabinet on transformation drive, ‘ be committed and sincere 

  By Suleiman Adamu, Sokoto SOKOTO state Governor Dr Ahmed Aliyu Sokoto has tasked members …

Leave a Reply

Your email address will not be published.