Home / News / 2023: Mun Amince Da Kalaman Kungiyar Dattawan Arewa, Cewa Shugabanci Ya Ci Gaba Da Zama A Arewa

2023: Mun Amince Da Kalaman Kungiyar Dattawan Arewa, Cewa Shugabanci Ya Ci Gaba Da Zama A Arewa

Mustapha Imrana Abdullahi
Gamayyar kungiyoyin fafutukar kare muradun mutanen arewacin Najeriya, CNG sun bayyana goyon bayansu da irin kalaman kungiyar Dattawan arewacin Najeriya ke yi, ta hannun mai magana da yawun kungiyar, Dokta Hakeem Baba – Ahmad cewa yankin arewacin Najeriya zai yi amfani da karfin kuri’ar da yake da shi domin ci gaba da mulkin har bayan shekarar 2023.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Gamayyar kungiyoyin da ke fafutukar Kwamared Abdul’Aziz Suleiman.
Inda takardar ta ci gaba da bayanin cewa hakika kalaman da mai magana da yawun kungiyar Dattawan arewacin Najeriya Baba – Ahmad  ya yi abin goyon baya ne don haka su na tare da wadannan kalamai.
Dokta Hakeem Baba – Ahmad dai ya yi maganar ne a lokacin da yake gabatar da bayani a wajen laccar tunawa da marigayi Dokta Mai tama Sule da bangaren daliban kungiyar CNG na jami’ar Ahmadu Bello zariya suka shirya, inda a wajen taron Baba- Ahmad ya bayar da misali da kalaman da wasu Gwamnonin yankin Kudu Sule yi na mulki ya koma Kudancin kasa.
A wadansu kalamai anlokuta daban – daban kungiyar CNG sun mayar da martani ga kalaman kungiyoyin al’ummar Inyamurai da na Yarbawa wato Ohanaeze” da “Afenifere” da kuma na yayan kungiyar mutanen yankin tsakiyar arewacin Najeriya na “MBF”, ga Baba- Ahmed, cewa arewacin Najeriya ba za su kara amincewa da duk wata barazanar kokarin yin batanci da yan siyasar yankin Kudancin Najeriya ke ganin ita ce kawai hanyar da ta rage su bi domin samu shugabancin kasa.
Takardar ta kungiyar CNG mai dauke da sa hannun mai magana da yawun kungiyar Abdul’Aziz Suleiman, ta ce ya zuwa yanzu kowa ya ga ne irin kalaman da ake yi cewa ayi tsarin karba karba da ya fito daga wasu jam’iyyu duk karya ne domin ba za a iya aiwatar da hakan a aikace ba musamman ma daga yan siyasar Kudancin Najeriya da kansu.
“Kamar yadda kungiyoyin yan kabilar Yarbawa, Inyamurai da na mutanen tsakiyar arewacin Najeriya suka Sani cewa sun dade su na lalata damar mutanen Arewa musamman ga dukkan yarjejeniyar da aka yi, don haka kowa ya shi ta fisshe shi kawai.
“Muna kuma tabbatar masu da cewa ba wani abin yin alfahari ba ne ga Gwamnonin kudu su koma yin kalaman bakin fenti da kuma neman balantana wani yankin da a fili take cewa su ne ke da yawa a siyasance babu wani boye boye”, Inji Suleiman.
Indai ana maganar samun dai- daito, adalci da kuma bin tsarin raba dai- dai, gamayyar kungiyoyin fafutuka sun gane cewa yankin Arewa ya rike shugabancin Najeriya ne na tsawon shekaru Takwas tun Dawowar tsarin mulkin Dimokuradiyya a shekarar 1999, don haka ya dace ayi tsarin adalci ga Arewa ta yadda za a samu raba dai- dai ta fuskar adalci.
“Saboda haka ne muke ganin cewa babu wani da zai yi kuskuren haifar da wani yanayi a kasa da zai kawo damewar al’amura a cikin kasa.
“Tun da dai Gwamnonin kudu sun zabi fitowa a fili su rika yin barazana da kokarin yi wa yankin Arewa bakin fenti don haka babu laifi ga yankin arewacin kasar ya tabbatar da karfin da yake da shi ta fuskar kuri’a a duk lokacin da zabe ya zo wanda jama’ar Arewa za su yi abin da suka yi da katinsu na zabe a shekarar 2015”, Suleiman na jaddawa don su ji da kunnensu.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.