Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’Aziz Yari Abubakar Shetiman Mafara, ya bayyana cewa sun amince da Dawowar Gwamnan Jihar Zamfara Mohammad Bello Matawalle jam’iyyar APC.
Abdul’Aziz Yari ya bayyana hakan ne a wajen babban taron yayan jam’iyyar APC da aka yi a garin Kaduna.
An dai yi wannan babban taro ne a garin Kaduna inda dimbin dubban yayan APC suka taru a Kaduna domin tattaunawa ta hanyar tuntubar Juna game da batun komawar Gwamnan Zamfara cikin jam’iyyar APC sakamakon ficewar da ya yi daga tsohuwar Jam’iyyarsa ta PDP.
“Kamar yadda kowa ya Sani biyu ta fi daya kowa na son karuwa a cikin Jam’iyyarsa don haka muna maraba da Gwamna ya dawo APC a Jihar Zamfara”.
A game da batun zamansa shugaban jam’iyyar APC na kasa kuwa da yake takara a halin yanzu sai Abdul’Aziz Yaro ya ce a duk cikin masu neman wannan kujera ta shugabancin APC a kasa baki daya, “hakika ni na fi kowa cancantar zama shugaban APC na kasa domin na zama sakataren jam’iyya,shugaban jam’iyya, na kuma zama cikin shugabanni na kasa, na zama dan majalisar tarayya, na zama Gwamna Shekara Takwas, har na zama shugaban kungiyar Gwamnoni ta kasa don haka wa ya fi ni cancanta?
Don haka ina nan rike da jama’a kowa ya san hakan kuma zan ci gaba da rike jama’a saboda ce jarin kowa a siyasance.