MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
A kokarin ganin an yi bikin ranar ma’aikata kamar yadda aka saba a kowace shekara an gudanar da addu’o’in neman ci gaba da taimakon Allah a masallaci da Coci a Jihar Kaduna.
Kamar dai yadda muka kawo maku rahoton cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne aka yi addu’a a Coci hakan kuma a yau Juma’a aka yi addu’a a masallacin Juma’a na Shaikh Saba Ahmad Al- Saba da ake kira SMC Kaduna.
An dai gudanar da addu’ar ne karkashin jagorancin Liman Malam Sani inda aka roki Allah neman taimako da jin kansa tare da ciyar da kasa gaba. An kuma nemi Allah ya yi mana maganin matsalolin da ake samu na rashin tsaro.
Da wakilin mu yake tattaunawa da shugaban kungiyar kwadago reshen Jihar Kaduna Kwamares Ayuba Suleiman, ya shaidawa manema labarai cewa an shirya wannan bikin ranar ma’aikata ta Bana da da kokarin yin wadansu abubuwa kamar yin addu’o’i a masallatai da Coci Coci sai kuma taron bita domin tattaunawa da fadakarwa ta hanyar gabatar da kasidu da kuma shirin kula da lafiyar jama’a kyauta a ranar Asabar inda a ranar Lahadi kuma za a yi babban taron yayan kungiyar kwadago a filin wasa na ABS da ke cikin garin Kaduna.
Da yake yin tariyar baya shugaban kungiyar kwadago reshen Jihar Kaduna Kwamared Ayuba Magaji Suleiman cewa ya yi sakamakon kokarin kungiyar yan kwadago ne ya sa har aka samu lokacin tashi daga aiki ba kamar yadda lamarin yake a can baya ba da ka fara aiki shikenan ba lokacin tashi, amma a yanzu kowa ya Sani awa Takwas ne ake tashi daga aiki da dai sauran muhimman ayyuka da dama da suka hada da nemawa ma’aikata da kasa yanci.