Home / KUNGIYOYI / A AREWACIN NAJERIYA AKWAI JAGORANCI – MUHAMMAD ALI

A AREWACIN NAJERIYA AKWAI JAGORANCI – MUHAMMAD ALI

….A hana yawon barace – baracen kananan yara a duk fadin Najeriya
DAGA IMRANA ABDULLAHI
DAN takarar neman kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya Honarabul Muhammad Ali ya bayyana yankin arewacin Najeriya a matsayin wurin da ke zaune kara zuba ba tare da samun shugabannin da za su yi masa jagoranci ba tun bayan rasuwar marigayi Sardauna Sa Ahmadu Bello da ya kawo ci gaban da ake takama da shi a halin yanzu.
Honarabul Muhammadu Ali, wanda masani ne a kan harkokin tsaro ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ga yayan kungiyar ‘Ayan Almajiri Empowerment Initiative’ da suka kai masa ziyara a ofishinsa da ke Kaduna.
“Ta yaya za a ce duk mutanen da suke a arewacin Najeriya har da wadanda ke a kan madafun iko a halin yanzu amma sun bari hatta irin abubuwan da Sardauna ya samawa yankin Arewa da suka hada da kamfanoni da sauran wadansu abubuwa a halin yanzu duk sun durkushe, ya bayar da misali da kamfanin wallafa jaridun “New Nigeria da Gaskiya Ta Fi Kwabo” wanda gaskiya ta fi Kwabo ce ta rika bayar da labarin Yakin basasar da aka yi a Najeriya kuma sanin kowa ne ba jaridar da take yi wa Gwamnati aiki irin wadannan jaridun guda biyu, sannan ko a can baya Gwamnati na yin amfani da matsayar jaridar ne a koda yaushe, amma a yau duk sun gurkushe babu labarinsu”.
“Saboda haka ya zama wajibi mutanen yankin arewacin Najeriya su farka daga baccin da suke yi, domin hakan ba zai kai su ga samun tsira ba ko ci gaban yaya da jikoki da suke zuwa a nan gaba”.
Da yake bayani a game da irin kokarin da kungiyar Ayana Almajiri Initiative ke aiwatarwa kuwa ya ce kokari ne mai kyau kuma mai fadin da zai ciyar da yankin Arewa da kasa gaba.
“Amma abin da muke bukata shi ne a hana yawace yawacen kananan yara da sunan bara a kan tituna, kasuwanni da wasu wuraren da bai kamata a ga yara a wurin ba , saboda ni ko a yau na halarci taron saukar karatun yara har na makaranta uku kuma abin sha’awa duk yaran sun yi karatu ne daga gidajen iyayensu”.
“Saboda haka ta yaya mutum zai haifi da ya kaishi yawon bara da sunan karatun Kur’ani domin me ba zai yi karatunsa a cikin gaban iyayen da suka haife shi ba sai a rabe da batun karatu ana kai yara manya gobe yawon barace barace?
Sai kuma wani abin da Muhammadu Ali ya gano cewa ana yi wa batun Almajirai jam’i ba tare da an rarraba ba shi ne ana kasa gane cewa akwai yaran da suke yin dakon daukar kayan jama’a musamman a tashoshin mota da wadansu wuraren taruwar jama’a kuma yaran nan ba musulmai bane, don haka abin da ya dace a kira abin shi ne yaran da suke gararamba a kan tituna.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin tarayyar Najeriya da ta mayar da hankali a game da inganta makarantu da hukumomin karatun Tsangaya da hukumar daukar jarabawar fita sakandare ta makarantun Allo da Islamiyya (NBAIS) da ke karkashin Gwamnatin tarayya domin inganta su zai kawo ma’ana kwarai.
Kuma nan gaba za mu kawo maku wadansu bayanan a kan abin da ya wakana lokacin ziyarar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.