Home / Kasuwanci / A Rika Amfani Da Kasuwar Duniya Ta Zama Sati Sati – Ahmad Dangiwa

A Rika Amfani Da Kasuwar Duniya Ta Zama Sati Sati – Ahmad Dangiwa

 Imrana Abdullahi
Shugaban Bankin bayar da lamunin gini, gyaran Gidaje na tarayyar Nijeriya Alhaji Ahmad Musa Dangiwa, ya yi kira ga hukumar da ke kula da kasuwar duniyar kasa da kasa ta Kaduna (KADCCIMA) da su duba yuwuwar yin amfani da wani bangare na kasuwar domin samun kudin shiga madadin a bar wurin sai shekara shekara.
Alhaji Ahmad Musa Dangiwa ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci cibiyar yan jarida da ke cikin Kasuwar, jim kadan bayan da ya halarci taron bikin ranar Bankin bayar da lamunin gina gidaje da aka yi a kasuwar da ke ci a wannan shekarar 2021 karo na 42 a mazaunin kasuwar na dindindin a Kaduna.
Alhaji Dangiwa ya ce hakika idan aka duba yin amfani da wannan kasuwar ta zama ana yin amfani da wani bangare na kasuwar a rika cin kasuwar a sati sati zai taimaka kwarai kasancewar wurin yana kusa da babban titin da ya hada Jihohi da dama.
“Ya dace a yi amfani da wannan kasuwar domin a rika zuwa ana cin kasuwar sati sati madadin a bar wurin haka kawai sai shekara shekara ake amfani da shi wajen cin kasuwa, in an aiwatar da wannan shawarar za ta taimaka kwarai kuma hukumar kasuwar za ta samu kudin shiga, wato dai za a amfana”, inji shi.
Dangiwa ya kara da cewa aiwatar da shawarar zai taimaka matuka ta fuskoki da dama wajen samun bunkasar tattalin arzikin kasa da jama’arta baki daya.
“Muna kuma ba wannan hukuma ta kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna shawarar su kara bayar da himma da kwazo wajen yin amfani da kafafen yada labarai domin fadakar da jama’a su kara fahimtar abin da ake yi a kasuwar da kuma dukkan lokacin da za a yi wani al’amarin da ya shafi harkokin kasuwar”, inji Dangiwa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.