Home / KUNGIYOYI / A Saukaka Farashi – Kalifan Tijjaniyya

A Saukaka Farashi – Kalifan Tijjaniyya

 

Daga Hussaini Yero, Funtua

Sakamakon zagayowar watan da aka haifi fiyayan Halita Annabi Muhammad Bin Abdullahi (saw) Kalifan Tijaniya Aliyu Saidu Alti Funfuwa,yayi kira ga ‘Yan Kasuwa da masu sana’ar hannu ,da masu jigilar ababan hawa da su saukaka farshin,sabo da murnar haihuwar Annabi Muhammad Muhammad .kuma yin haka zai bunkasa arzikin su.

Kalifa Ali Saidu Alti ya bayyana haka ne
a ranar Asabar da tagabata , 5/3/1444 ,Watan rabiul Auwal wanda yayi daidai 1/10/2022, ga Mahalarta Taron Dalibai sama da Miliyan Daya da dari da suka Halarci zagayan Maulidi, Karkashi Jagorancin Zawuyar Shek Abubakar Alti Funfuwa, cikin Jihar Katsina.

Shugaban Kwamitin zagayan garin Maulidin, Bashir Muhammad ( KIN) ne ya bayyana addadin Dalibai da Malamai da suka Halarci zagayan garin Maulidin karu na farko , a wajan taron.

Bishir Muhammad ya bayyana cewa, Sama da Makarantun Allo da na Islamiya 489 na yankin Funtua da wasu Makarantun daga Jahohin , Zamfara, Kaduna da Kano ne ke halartar zagayan garin Maulidin Mazan Allah (saw) da ake yinsa duk shekara. Inji Shugaban Kwamitin.

Anasa Jawabin Shugaban makarantar Hizbu Rahim Funtua Ustas Salisu Tasiu ya bayyana cewa,Shekaru Arbain ke nan da fara wannan Zagayan Maulid da Islamiya Daya da kuma ‘yan tsirarun Dalibai cikin ikon Allah gashi yanzu milyoyine ke halarta zagayan daga jahohi daban daban. Inji Ustas Salisu Tasiu.

“Ustas Salisu Tasiu ya Kuma kara da cewa, Dalibai da Malamai ne ke fitowa cikin kyawawan shiga dan taya Manzan Allah (saw) murnar zagayowar watan da aka haifeshi. Akan haka ne muke godema Allah da ya sanyamu cikin masoyan Sayyidina Rasulullahi(SAW).

Anasa Jawabin Kalifa Ali Saidu Alti ya bayyana cewa, Maulidin Mazan Allah (Saw) hidimace da kowa da kowa kuma hidimace ta Manzan Allah (saw) dan haka wajibine garemu mu fito Mazanmu da matanmu mu nuna ma duniya mu masoyan Sayyidina Rasulullahi (SAW) duniya ta sheda muna tare dan Manzan Allah jiki da jini munbada ga Manzan Allah ( saw ).

“Kalifa ya kara da cewa,wannan watane na Manzan Allah wanda kowane Mutum akwai murnar da zaibayya ma Allah musamman na Sadaukarwa ga Sana’arsa ga Manzan Allah (saw) akan hakane na ke kira ga Yan Kasuwa dasu saukaka farshin abunsaidawar ga al’umma albarkaci Manzan Allah (saw) suma masu abubuwan hawa na Motoci da Mashina su saukaka farshin ko su ware Wani lokaci da zasu dauke Mutane kyauta albarkascin Manzan (Allah) .
Kuma duk wanda yayi Wannan lallai zaga budi a wajan kasuwancin sa.inji Kalifa.

Ma’ajin Kwamitin zagayan Maulidi , Alhaji Bashir Yero,ya bayyana godiyar sa da Sadaukarwar ‘Yan Kwamitin sukeyi dan ganin angudanar da shi lafiya.

Suma sauran Mutane ‘Yan kasu da masu mukaman siyasa da suka bamu gudunmuwa muna godiya agare su.

About andiya

Check Also

Gwamnatin Hadin Kan Jama’a Na Haifar Mana Da Nasara – Gwamna Uba Sani

  …Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri Daga Imrana Abdullahi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.