Home / News / Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamnan Jihar Zamfara

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamnan Jihar Zamfara

APC SAK MATAWALLE GA ZAƁINMU SARKIN SHANUN SHINKAFI MUKE SO
Daga Honarabul Abubakar Lauwali kaura Shinkafi
Zuwaga mai girma Gwamnan Jahar Zamfara Shatiman Daular Usmaniyya khadimul ƙur’an, Dokta Bello muhammad matawalle ardenB Qasar Hausa.
Daga matasa da Dattawan  ƙaramar hukumar mulkin shinkafi bisa jinjina da kuma sosayya da ƙauna da Kake wa al’ummar ƙaramar hukumar mulkin shinkafi a bisa wannan dalilin ne mu al’ummar Shinkafi muke durƙusar da kan mu gare ka Mai girma Gwamna muna roƙo, kuma muna bara sannan  muna son da ka taimakemu kabamu Dokta sulaiman Shu’aibu Shinkafi sarkin Shanun shinakafi na farko a matsayin shugaban  ƙaramar hukumar mulkin shinkafi don darajar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihin wasallam, domin wallahi mai girma Gwamna Wannan mutumin ne ɗai zaka bamu a huta da rigime rigime da ke tashi a ƙaramar hukumar mulkin  Shinkafi.
Mai Girma Gwamnan wallahi Wannan roƙon da muke son Allah ya samu a hannu kaima kasa mana hannu alkhairi ne gare mu baki ɗayanmu da ke ƙaramar hukumar mulkin shinkafi, duba da yadda abubuwan ƙaramar hukumar mulkin shinkafi suka lalace da taɓarɓarewar Jam’iyar tamu ta APC.
Mai Girma Gwamna ahalin yazu lungu da saƙo babu inda alkhairin Dokta sulaiman Shu’aibu Shinkafi bai kai ba haka zalika wallahi  mai girma Gwamna ahalin yanzu Dr sulaiman Shu’aibu Shinkafi ya zama uba da uwa  ga dukkan Illahirin matasan garin ƙaramar hukumar mulkin shinkafi don sama da samari 3000 ya taimaka wurin samun abun dogaro da kai wanda ya haɗa da babura, Kwamfutoci, injunan Markade, Injunan Taliya da kuma bayar da tallafin kuɗi ga al’ummar,
Bugu da ƙari mai Dokta sulaiman Shu’aibu Shinkafi Sai da ya bi assibitoci tun daga babban asibiti ya na bada tallafin kuɗi tare da magunguna don taimakawa ga Gajiyayyu marassa ƙarfi a cikin al’umma.
Mai Girma Gwamna yakamata a duba mana Wannan, a kan haka muke roƙo kuma muke bara da a taimakemu don wallahi Shinkafi ko ina sarkin Shanu suka so kuma shi ne zaɓin mu kuma shi ne zaɓen al’umma.
Da fatan wannan saƙon mai girma Gwamna za’a dubemu da shi da idon rahama Mungode daga ɗinbin al’ummar ƙaramar hukumar mulkin shinkafi tun daga dattawa, matasa, malammai da almajirai faƙirrai suka bada shawarar a rubuta wannan saƙon zuwa gareka.
Mungode.
Daga Honarabul Abubakar Lauwali kaura Shinkafi

About andiya

Check Also

Trafficking: NAPTIP seeks more collaboration, advise potential victims

  By Suleiman Adamu, Sokoto The National Agency for the Prohibition of Trafficking in Person(NAPTIP) …

Leave a Reply

Your email address will not be published.