Home / News / ABDUL’AZIZ YARI YA CANCANCI ZAMA SHUGABAN MAJALISAR DATTAWA – Bashir Nafaru

ABDUL’AZIZ YARI YA CANCANCI ZAMA SHUGABAN MAJALISAR DATTAWA – Bashir Nafaru

DAGA IMRANA ABDULLAHI

An bayyana tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma tsohon shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya Alhaji Abdul’Aziz Yari Abubakar Shetiman Mafara a matsayin wanda ya cancanci zama shugaban majalisar Dattawan Najeriya.

Alhaji Bashir Nafaru ne ya bayyana hakan a lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a wayar Salula.

Bashir Nafaru ya ce ” Hakika Shetiman Mafara Alhaji Abdul’Aziz Yari ya cancanci ya zama shugaban majalisar Dattawa kasancewarsa mutum ne mai son taimakon jama’a a koda yaushe. Kuma ya yi bayanin cewa ya na son magance matsalolin tsaro, taimakawa yan gudun hijira kowa ya samu muhalli ya zauna a cikin gidansa tare da iyalansa da kuma yin aiki a game da batun bambancin addini da wasu ke amfani da shi a kasa”.

Saboda haka duk mai irin wadannan kudirorin na alkairi da za su ciyar da kasa gaba ya dace ya zama shugaban majalisar da su ne keda alhakin yin dokoki na kasa.

Kuma kamar yadda kowa ya Sani tun daga garin Talatar Mafara zuwa Jihar Zamfara da kasa baki daya kowa ya san irin taimakon da yake yi wa jama’a domin kara inganta rayuwarsu a koda yaushe.

Idan dai za a iya tunawa kadan daga cikin irin kokarin wannan bawan Allah akwai aikin da ya aiwatar a watan Azumin da ya gabata da ya rabawa jama’a tirelolin abinci har guda dari biyu da Arba’in  (240) wanda aka kaddamar a garin Talatar Mafara kuma aka rabawa kananan hukumomin Jihar Jihar sauran yan kungiyoyi da duk wanda Allah ya tsaga da rabon ya samu, don haka wannan mutum ne da ya cancanci ya zama shugaban jama’a baki daya ba ma a majalisa ba kawai.

About andiya

Check Also

Northern govs meet in Kaduna, design regional economy, human capacity devt

    The chairman, Northern States Governors’ Forum (NSGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, has called for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.