Home / News / JAM’IYYAR LEBO TA DAKATAR DA JIGA – JIGAN YAYAN TA A KADUNA

JAM’IYYAR LEBO TA DAKATAR DA JIGA – JIGAN YAYAN TA A KADUNA

Jam’iyyar Lebo daya ce a Jihar Kaduna

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Shugaban jam’iyyar Lebo ta kasa reshen Jihar Kaduna Alhaji Auwal Ali Tafoki, ya bayyana cewa sakamakon irin yadda wadansu yayan jam’iyyar suke aiwatar da ayyukan da suka sabawa jam’iyyar yasa suka dauki matakin Dakatar da su baki daya.

Alhaji Auwal Ali Tafoki ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron da suka gudanar na masu ruwa da tsaki da ya gudana a garin Kaduna.

Tafoki, ya shaidawa shugabannin jam’iyyar Lebo da suka halarci taron tun daga matakin kananan hukumomi da sauran wasu masu ruwa da tsaki cewa a halin yanzu fa batun jam’iyyar Lebo sai dai kawai ayi gaba kuma duk mai son ayi tafiyar da shi ya hanzarta rungumar tafiya domin ba gudu ba ja da baya.

” Akwai masu son ayi tafiyar da su kuma akwai wadanda ma ke son su shigo cikin jam’iyyar Lebo a halin yanzu, saboda da haka ne muke cewa kodai ka na tare da mu ko kuma ka kasance can a wani wuri mu tafiya kawai muka Sani ba ja da baya”, inji Auwal Tafoki.

Ya kara da cewa muna da jam’iyyar Lebo guda daya ne a Jihar Kaduna don haka ba wani lokacin da za a bata sam- sam. Kuma jam’iyyar Lebo da kuke gani a halin yanzu ita wannan da ke dakin taron nan da muke ciki, don haka babu wata can daban sai wannan kawai.

” Babu wata ko wani da zai iya kiran shugabannin jam’iyyar Lebo guda 23 kamar yadda muke tare a halin yanzu ga shugabannin mata, Sakatarorin jam’iyya da duk sauran jigogin jam’iyyar 23 kamar yadda muke a nan saboda haka kada wani ya rude ku da wata magana ba wani bangaranci jam’iyyar Lebo guda daya ce kawai”.

Kuma a wannan wuri muna tare da dan takarar Gwamnan jam’iyyar Lebo da ya tsayawa jam’iyyar takara  a zaben da ya gabata, saboda haka ba inda za a ga dan takarar da ya tsayawa jam’iyyar Lebo takarar Gwamna sai dai a nan kawai.

Saboda haka kada kowa ya girgiza muna kan samun nasara. Kuma za mu kare bukatu da dukkan muradunku baki daya.

” Ko a satin da ya gabata wasu yayan jam’iyyar Lebo, sai kawai suka yanke hukunci zuwa su halarci wani haramtaccen taron masu ruwa da tsaki a garin Bauci hedikwatar Jihar Bauci  da sunan taron na kasa. Kuma a lokacin ni kaina ina halartar baban taron jam’iyya na kasa da muka yi a Abuja, amma wai sai ga su can a garin Bauci da suka kira Jihohi biyu kawai da suka hada da Bauci da Gombe dukkan sauran Jihohi 34 suna garin Abuja suna halartar babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar tare da shugabanni na kasa Barista Julius”, inji Auwal Tafoki.

” Ba tare da yin kuskure ba hakika duk wannan na faruwa ne domin kawai ya kawo wa tsarin da muke ciki na shari’a tangarda saboda dukkan mu kowa ya Sani cewa dan takarar shugaban kasa Dokta Peter Obi ya lashe zabe saboda daga na’urar da aka yi zabe hakan ya bayyana cewa Peter Obi ya lashe zabe. Kuma mun gano cewa lokacin da duka fara yin magudi ne suka rika rubutawa yan takara yawan kuri’un da suke son ba su duk hakan ya bayyana fili karara”.

Auwal Tafoki ya kuma yi zargin cewa jam’iyya mai mulki ce ke daukar nauyin wadansu mutane a cikin jam’iyyar Lebo da sunan yayan jam’iyyar domin kawai su zama shugabannin jam’iyyar wanda nan gaba za su ce ai sun janye karar da ake yi ta zaben shugaban kasa da aka yi da a yanzu aka kai kara kotun sauraren karar zabe, wanda da ikon Allah hakan ba za ta yuwu ba”, duk inji Auwal Tafoki.

About andiya

Check Also

Northern govs meet in Kaduna, design regional economy, human capacity devt

    The chairman, Northern States Governors’ Forum (NSGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, has called for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.