Home / News / Abin Da Gwamnan Zamfara Ya Yi Dai- dai Ne – Yusuf Shitu Galambi

Abin Da Gwamnan Zamfara Ya Yi Dai- dai Ne – Yusuf Shitu Galambi

Mustapha Imrana Abdullahi
An bayyana matakin da Gwamnan Jihar Zamfara ya dauka na ficewa saga cikin jam’iyyar PDP zuwa APC da cewa shi ne mafi alkairi da dacewa, a baki dayan tafiyar siyasarsa.
Honarabul  Yusuf Shitu Galambi, dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Gwaram ne ya bayyana hakan lokacin da yake ta ya Gwamnan Jihar Zamfara murnar dawo da Jihar wurin da ya dace ta fuskar siyasar kasa, kasancewar ya dawo da Jihar Zamfara ta shiga jerin jam’iyyar da ta kasance ta kasa baki daya.
A cikin wata takardar da dan majalisa Yusuf Shitu Galambi ya rabawa manema labarai inda ya ce komawar Gwamna Matawalle hakika ya ba Jihar damar komawa cikin jerin jihohi shida na yankin Arewa maso Yamma da suka kasance karkashin APC wanda PDP ta kasance da guda daya tilo.
Honarabul Galambi wanda yake da sarautar gargajiya ta Ajawan Dutse, a Jihar Jigawa ya bayyana shigar Gwamna Matawalle cikin PDP a matsayin wata kyauta daga Allah madaukakin Sarki da ya kawowa Jihar kwarjini da karin bunkasa.
“A matsayin Gwamnan na aboki da muka yi majalisar wakilai tare, hakika ya bayyana irin jajircewarsa,hakuri da juriya tare da kwazon aiki ga tausayi da sanin yakamata mai kokarin yin tsari ga dukkan al’amuran da ya Sanya a gaba, da ya kasance a koda yaushe ya kawo ci gaba a mazabarsa ne burinsa”. Galambi ya tabbatar da hakan.
Dan majalisar sai ya yi kira ga Gwamna Bello Matawalle da ya nuna halin yakamata a matsayinsa na shugaban jam’iyya  a Jihar da hanyar rungumar kowa da kowa ayi aikin ciyar da Jihar gaba wanda yin hakan zai kai Zamfara ga samun karin daukaka zuwa mataki Naga ba.
Galambi ya ci gaba da bayanin cewa kasancewar irin yadda yayan jam’iyyar PDP ke karara zuwa APC alama ce da ke nunin cewa APC na kan gaba a zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Sai Galambi ya yi wa Gwamna Matawalle jinjina bisa matakin da ya dauka na komawa jam’iyyar da ke kan gaba a Najeriya wato APC.
Ya kuma yi kira ga daukacin jama’ar Jihar Zamfara da su ci gaba da ba Gwamnan cikakken hadin kai da goyon baya domin ya samu sukunin ciyar da Jihar gaba, tun da dai ya shiga jam’iyyar da masu ra’ayin ci gaba suke.
Galambi ya kuma mika godiyarsa ga kwamitin APC da ke shirya babban taron da APC za ta yi na kasa karkashin Gwamnan Jihar Yobe, Gwamna Mai Mala Buni, da cewa abin da suke yi abin a ya ba ne wanda sakamakon hakan ake samun kyakkyawan tsarin karbar yayan jam’iyyar wadansu yayan jam’iyya shiga cikin APC.
Ya kuma ya ba wa irin kokarin da shugaba Muhammadu Buhari da kuma Gwamnoni masu ci gaba da suka kasance komai ya zama cikin kwanciyar hankali da lumana da zai taimaki dukkan masu tasowa nan gaba.

About andiya

Check Also

Majalisar Wakilai: Sani Jaji Zai Maye Gurbin Abbas Tajuddeen?

Daga Imrana Abdullahi Kamar yadda wadansu bayanai suka bayyana a kafar yada labarai ta jaridar …

Leave a Reply

Your email address will not be published.