Home / News / ALLAH YA FITAR DA MU KUNYAR JAMA’A – DAUDA LAWAL DARE

ALLAH YA FITAR DA MU KUNYAR JAMA’A – DAUDA LAWAL DARE

 

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Sabon zababben Gwamnan Jihar Zamfara karkashin jam’iyyar PDP Dokta Dauda Lawal Dare ya bayyana cewa da ikon Allah jama’a za su ga sabuwar Jihar Zamfara ta bangarorin rayuwar al’umma daban daban.

 

Ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da kafar yada labarai ta bbc hausa. Inda ya ce hakika akwai shi da ingantattun tsare tsaren ciyar da rayuwar al’ummar Jihar Zamfara da Najeriy gaba, kuma za a gansu nan ba da dadewa ba da ikon Allah.

 

“Za mu yi kokarin a fannin tabbatar da ingantaccen tsaro, Lafiya, ilimi da sauran fannonin samar da abubuwan more rayuwar jama’a da ban daban, da wannan ne muke yin addu’ar Allah ya fitar da mu KUNYAR jama’a da suka tashi tsaye wajen zaben mu”.

 

A game da yawan kuri’a da kuma kananan hukumomin da ya samu kuwa ya yi wa Allah godiya da ya bashi wannan gagarumin rinjaye, inda ya ce ko da a yanzu idan za a yi kididdiga su dayan bangaren na Gwamnati ba su samu yawan kananan hukumomin da suke cewa sun samu ba,domin Iowa ya san muke da rinjaye”.

About andiya

Check Also

GWAMNATIN TINUBU TA WUCCIN GADI CE – ATIKU

Daga Imrana Abdullahi A wani kokarin kara fadakar da dimbin yayan jam’iyyar PDP mutumin da …

Leave a Reply

Your email address will not be published.