Home / Labarai / Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Hukumar Kwastan Dikko Inde Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Hukumar Kwastan Dikko Inde Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Hukumar Kwastan Dikko Inde Rasuwa
Mustapha Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga garin Musawa Jihar Katsina sun tabbatar mana da cewa Allah ya yi wa tsohon shugaban hukumar kwastan ta kasa Alhaji Dikko Abdullahi Inde rasuwa.
Kamar yadda majiyar ta shaida mana cewa daman ya sha fama da rashin lafiya har zuwa lokacin da ka’ida ta yi cikin hukuncin Allah.
A tarihi dai marigayin shi ne mutumin da ya rika daukar yayan Talakawa aiki a hukumar kwastan da ya shugabanta karkashin Gwamnatin PDP a tarayyar Nijeriya ba tare da sun bayar da ko Kwabo ba.
Kuma a lokacin da yake shugabancin hukumar ko tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan na yaba masa irin yadda yake gudanar da aiki har wasu lokutan ma hukumar ke tara kudin da ake yin Albashi a kasar.
Allah dai ya gafarta masa ya kuma albarkaci abin da ya bari.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.