Al’ummar Jihar Zamfara sun bayyana rashin jin dadinsu bisa irin halin kuncin da suka shiga ciki sakamakon rashin Sabis din wayar Sadarwa a wasu Jihohin jihar musamman ma a yankin Shinkafi da Kauran Namoda.
“A birnin Magaji da Shinkafi duk babu sabis na kamfanonin wayar mtn,Etisalat,Airtel da Glo kuma hakan ya sanya yau kusan sati biyu ban yi magana da iyaye na ba domin ba data kwata kwata. Kuma a matsayin mu na yan Najeriya, yan jihar Zamfara kuma yan Adam duk muna da yancin a ba mu sabis domin mu yi amfani da shi wajen sadarwa da yan uwa sannan muna da yanci a ba mu sabis na data domin yin huldar yanar gizo da yan uwa da abokan arziki, sakamakon hakan kasuwancin mu ya tsaya ba zumunci Sam duk abin da muke ciki ba za mu iya yin magana da kowa ba”.
Sai dai kawai yau a sace wannan gobe a kashe wancan ba yadda zaka iya gaya wa duniya halin da ake ciki ba sabis na data ba na magana, don haka muna yin kira ga gwamnatin tarayya da ta ja hankali tare da Jan kunnen hukumar kula da kamfanonin Sadarwa ta NCC, kuma su NCC din su ja kunnen kamfanonin Sadarwa na Mtn, Airtel, Etisalat da glo domin su yi gaggawar mayar da sabis na sadarwa a kananan hukumomin Shinkafi, Zurmi, Kauran Namoda da Birnin Magaji.
” Muna fama da rashin sadarwa da rashin kasuwanci muna fama da kashe kashe ga dai masifu iri – iri duk sun taru a wannan yankin”.
” Hakan ya sa muke yin kira ga al’ummar Kasashen waje da su kawo dauki ga wannan jama’r yankunan da muka zayyana, muna cikin masifa da bala’i.
A hakan ne muke shaidawa Gwamna Dauda Lawal da ya hanzarta shiga cikin wannan batu a mayar wa al’umma sabis ta yadda zs su iya yin magana da yan uwansu domin su shaidawa yan uwansu wadanda aka sace da wadanda suka rasa rayuwarsu ga kuma hanya ba kyau.
“Saboda haka a rika cewa wai ana yin yaki ne duk magana ce kawai ga hanya ba kyau sai suka yi kira ga gwamnati da kada su sake a cimma kisisinar rage yawan mutane a boye.
A halin yanzu ba Lafiya ba makaranta ba kuma ziyarar yan uwa komai ya tsaya domin ba sadarwa.
Muna yin kira ga Gwamnatin jihar Zamfara da ta mayar wa jama’a da wannan sabis, in ba haka ba za mu kai dukkan wadannan kamfanonin Sadarwa da hukumar NCC kotun da take da hurumin sauraren mu domin tabbatar mana da yancin da muke da shi.
” Mun sani cewa an ga yankin APC ne ba wata jam’iyya ba shi ya sa ake kokarin yi mana wannan a Jefa mu cikin wahala don haka ba za mu yarda a siyasan tar da yancin mu ba da rayukan mu ba don haka dole ne mu tashi tsaye a kan wannan yakin na kwatar yancin.
Ina yin kira ga jama’ar kananan hukumomin Shinkafi,Birnin Magaji, Zurmi da Kauran Namoda da su ci gaba da tsaya wa da addu’a.
” Mun kuma ba Jihar Zamfara da wannan hukuma ta NCC da Kamfanonin nan kwanaki Bakwai in ba su yi wannan aiki na mayar da Sabis din sadarwa ba za mu kai su kotu domin neman yanci
THESHIELD Garkuwa