Home / Labarai / An Mika Sunan Sanata Hassan Nasiha Ya Zama Mataimakin Gwamnan Zamfara

An Mika Sunan Sanata Hassan Nasiha Ya Zama Mataimakin Gwamnan Zamfara

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI

SANATA Hassan Muhammad Nasiha, mai wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya ne aka mika sunansa ga majalisar dokokin Jihar Zamfara domin tantancewa ya zama mataimakin Gwamnan Jihar

Hakan dai ya faru ne biyo bayan tsigewar da majalisar dokokin Jihar ta yi wa tsohon mataimakin Gwamna Mahadi Aliyu Muhammad Gusau, a ranar Laraba.

Mahadi dai yan majalisar sun Tsige shi ne biyo bayan rahoton da kwamitin bincike ya aiwatar inda aka same shi da laifi a kan maganar kudi

Bayan da majalisar ta dawo domin zamanta, shugaban majalisar Nasiru Mu’azu, ya karanta takardar da Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya aiko wa majalisar inda ya rubuto cewa ya zabi Sanata Hassan Muhammad Nasiha a matsayin mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara.

About andiya

Check Also

Interfaith Harmony Week 2023; Christians- Muslims Mobilize Preachers to offer Special Prayer, Fasting for God to end Russian /Ukraine War

  A head of This year 2023 world United- nation international interfaith week and harmony …

Leave a Reply

Your email address will not be published.