Home / News / BA RUWAN MU DA TSARIN KARBA KARBA – GBENGA OLAWEPO HASHIM

BA RUWAN MU DA TSARIN KARBA KARBA – GBENGA OLAWEPO HASHIM

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI

TSOHON dan takarar neman kujerar shugabancin kasar nan Gbenga Olawepo Hashim, ya bayyana cewa zaben mutane nagari masu kishi da sanin yakamata ne mafita ga yan Najeriya ba batun tsarin zaben karba karba ba da wadansu ke kokarin cusa wa jama’a.

Gbenga Olawepo Hashim, ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan gabatar da kasida mai taken kokarin Uthman Danfodiyo wajen yaki da cin hanci da rashawa, da ya gabatar a dakin taro na gidan tunawa da sa Ahmadu Bello Sardauna.

Gbenga ya ci gaba da cewa “ba ruwan mu da tsarin karba karba saboda haka ne muke yin kira ga daukacin al’umma da su kula da zaben mutanen kirki masu kishin kasa da son ci gaba, amma ba batun karba karba ba”.

“Muna son wadanda za su shiga zabe har jama’a su zabe su da suka kasance masu kokarin kawo ci gaban da kowa zai amfana a samu ingantaccen tsaro da kawar da yunwa da talauci kowa ya ji dadi sosai don haka ba ruwan mu da batun karba karba a maganar wanda za a zaba domin zama shugaban kasa”.

Gbenga ya kara fadakar da jama’a game da irin halayyar da ake ciki na rungumar batun cin hanci da karbar rashawa a tsakanin al’ummar kasa, abin da ya bayyana da cewa mafi akasarin jama’a a halin yanzu duk sun yi na’am da batun cin hanci da karbar rashawa har matasa na ganin kamar wani abu ne mai kyau.

“Hakika tsarin samun gaskiya da inganci a kan al’amura ya rushe tun da dadewa don haka duk mun karbi tsarin karbar rashawa, saboda haka sai mun dawo daga Rakiyar dukkan wadanda suka kasance sun gurbata da batun rashawa a kowa ne irin mataki wanda hakan zai bayar da damar samun tsari mai inganci da ake bukata a canza tsarin da ke cikin al’umma mara kyau. Muna kira ga daukacin jama’ar da suka taru a wannan waje da kowa ya yi kokarin mika wannan sakon ga duniya musamman ta hanyar yin amfani da yanar Gizo domin jama’a kowa ya fadaka kan batun a daina sace sacen duniyar jama’a a kowane irin mataki”, inji Gbenga.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.