Daga Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Dokta Dikko Umar Radda ta aike da sunayen mutane 20 domin a nada su mukaman kwamishina.
Kamar yadda wata takardar da ke dauke da sa hannun Maiwada DanMallam Darakta Janar mai kula da harkokin kafofin yada labarai a ofishin Gwamnan Jihar ta bayyana cewa an aike da sunayen ne ga majalisar dokokin Jihar Katsina domin amincewa da su kafin Gwamnan ya Rantsar da su matsayin kwamishinoni.
Ga dai sunayen nan kamar haka;
1- Professor Ahmed Muhammad karamar hukumar Bakori
2-Hon Ishaq Shehu Dabai- karamar hukumar Danja
3- Associate Professor Badamasi Charanchi – karamar hukumar Charanchi
4-Dr. Nasir Muazu Danmusa- karamar hukumar Danmusa
5- Malam Bala Salisu – Zango karamar hukumar Zango
6- Professor Ahdulhamid Ahmed- karamar hukumar Mani
7-Hon. Musa Adamu Funtua- karamar hukumar Funtuwa
8-Alh Yusuf Rabiu Jirdede- karamar hukumar Maidaua
9-Hon. Aliyu Lawal Zakari- karamar hukumar Dutsi
10- Hon. Bishir Tanimu Gambo —karamar hukumar Dutsinma
11- Bariister Fadila Muhammad Dikko — karamar hukumar Kurfi
12-Hon. Hamza Sulaiman- karamar hukumar Faskari
13-Alh. Isah Muhammad Musa- karamar hukumar Kankara
14-Eng. Dr. Sani Magaji – karamar hukumar Ingawa
15-Dr. Faisal Umar- karamar hukumar Kaita
16- Alh. Bello Husaini Kagara- karamar hukumar Kafur
17- Dr. Bishir Gambo Saulawa- karamar hukumar Katsina
18-Hajiya Hadiza Yaradua- karamar hukumar Katsina
19-Hajiya Zainab M Musawa – karamar hukumar Musawa
20-Alh. adnan Nahabu – karamar hukumar Daura
Dukkan sunaye nan na mutane 20 na jiran majalisar dokokin Jihar Katsina ne ta tantance sunayen.
Sai dai daga cikin sunayen akwai sunayen akalla mutane uku daga cikin sunayen mutanen 20 da suka yi kwamishinoni a cikin Gwamnati karkashin tsohon Gwamna Aminu Masari a Jihar amma duk karkashin jam’iyyar APC.