Related Articles
An Nada Sabon Shugaban Sojojin Nijeriya
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugabannkasa Muhammadu Buhari ya sanar da nadin sabon shugaban sojojin Nijeriya da ya sanar da sunan Mejo Janar Farouq Yahaya.
Mejo Janar Yahaya ya maye gurbin marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da ya rasu sakamakon hadarin Jirgin sama a kusa da filin Jirgin a ranar Juma’ar da ta gabata, a wata takardar sanarwar da ke dauke da sa hannun mai rikon mukamin Daraktan yada labarai na rundunar sojan Nijeriya janar Onyema Nwachukwu da ya fitar a ranar Alhamis ta bayyana cewa an nada Mejo Janar Yahaya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa kafin nadin nasa Mejo janar Yahaya shi shugaban rundunar soja ta daya kuma ya na aiki a matsayin shugaban rundunar soja da ke yaki da masu yan Ta’adda a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya rundunar mai suna Hadin Kai.