Home / KUNGIYOYI / An Yi Kira Ga El – Rufa’i Ya Gargadi Masu Kokarin Rushe Tashoshin Mota

An Yi Kira Ga El – Rufa’i Ya Gargadi Masu Kokarin Rushe Tashoshin Mota

An Yi Kira Ga El – Rufa’i Ya Gargadi Masu Kokarin Rushe Tashoshin Mota
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar Direbobi ta kasa NURTW reshen Jihar Kaduna Alhaji Aliyu Tanimu Zariya ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i da ya gargadi hukumar kula da gine gine ta Jihar da ke rushe tashar mota ba tare da yi wa dimbin jama’a tanajin wurin da za su zauna domin ci gaba da sana’o’insu ba.
Alhaji Aliyu Tanimu Zariya, ya yi wannan kiran ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kaduna.
Shugaban NURTW reshen jihar Kaduna ya shaidawa manema labarai cewa su a koda yaushe masu yin biyayya ne ga Gwamnati don haka suke bayar da shawarar cewa idan za a rushe Tashar mota to ayi kokarin samawa dimbin yayan kungiyar da ke neman abin da za su ci tare da iyalansu wurin da za su koma domin ci gaba da sana’arsu.
“An rushe tashar unguwar Talbishin da ake kira talbishin/ Kakuri, bayan an rushe sai aka ce masu su koma KSTA amma kuma wanann wuri ba gyara, ba wutar lantarki,ba ruwa, ba tsaro, saboda haka ta yaya jama’a za su kai dukiyarsu a wannan wuri. Ko su yayan kungiyarsu su koma domin ci gaba da gudanar da sana’arsu a wurin
Ya ci gaba da cewa ga shi kuma an rushe tashar Kantin kwari, amma duk mun gayawa mambobinmu su ci gaba da gudanar da aikinsu ana taimakon fasinjoji in sun zo a saka su a mota su ta fi inda suke bukata kamar yadda aka saba har sai Gwamnati ta tanadar mana wurin da zamu tsuguna”, inji Aliyu Tanimu Zariya.
Alhaji Aliyu Tanimu Zariya ya kuma bayyana goyon bayansa ga Gwamnatin Jihar wanda dalilin hakan ne ma yasa suke kokarin sayar da rasidin Gwamnati a dukkan tashoshin motocin da yake suna gudanar da sana’arsu ta tuki tsawon shekaru da dama.
“Muna kuma maraba da shirin Gwamnati ta kokarin duba lafiyar direbobi idan lokacin hakan ya zo, amma muna jiran umarnin uwar kungiya ta kasa a kan wannan batu”.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.