Home / News / Ana Ci Gaba Da Kada Kuri’a A Bakori

Ana Ci Gaba Da Kada Kuri’a A Bakori

Ana Ci Gaba Da Kada Kuri’a A Bakori

Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar dai yadda muka fara gaya maku tun da safiyar yau Asabar a garin Bakori da ke Jihar cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta raba kayan zabe cikin lokaci, a ahalin yanzu karfe 12: 17 jama’a na ci gaba da kada kuri’unsu domin zaben Dan majalisar dokoki ta tarayya daga karamar hukumar Bakori.
Kamar yadda wakilinmu ya zagaya wadansu mazabu ya gano irin yadda wadansu wurare jama’a suka yi tururuwa domin sauke nauyi kasancewarsu yan kasa masu yancin Jefa kuri’a suna ta aiwatar da yancin da tsarin mulkin kasa ya ba su.
Babban abin jin dadi a wannan zabe dai shi ne ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin ana yin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana, wanda hakan ke tabbatar da za a samu kammala zaben lafiya, da kowa ke bukata.

About andiya

Check Also

The Daily Hug For Appreciation 2023

The daily hug for 28/11/23 is this appreciation of an echo shared by my dear …

Leave a Reply

Your email address will not be published.