Home / Labarai / An Zargi PDP Da Ayyukan Ta’addanci A Jihar Zamfara

An Zargi PDP Da Ayyukan Ta’addanci A Jihar Zamfara

Gamayyar Kungiyoyin Kwararru Na Dattawan Arewa Sun Kalubalanci Kalaman PDP A Game Da Batun Tsaron Jihar Zamfara
…Sun Kalubalanci Dan takarar Gwamna Da Batun Raina Kotu Da Rashin Kwarewa.
Gamayyar Kungiyar kwararru Dattawan arewacin Najeriya ta (NEPGO), reshen Jihar Zamfara sun yi Allah wadai da kakkausar murya bisa kalaman da aka danganta jam’iyyar PDP da su na game da zargin kaiwa wasu yayan ta hari da aka danganta da batun irin rikicin siyasar da yake addabar jam’iyyar sakamakon batutuwan da suka Dabai baye jam’iyyar a Jihar.
Bauanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Kodineta na shiyya na gamayyar kungiyoyin Barista Lawal Murtala Zawiyya da aka rabawa manema labarai.
Gamayyar yayan kungiyar sun bayyana batun da cewa ba wani abu bane illa kamar Dora laifi a inda bai dace ba, saboda rashin Sani da ya haifar da zumudi ta rashin sadarwa mai kyau da gangan domin kawai ya lalata irin yanayin zaman lafiyan da ake samu a Jihar Zamfara.
Kalaman PDP wanda sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Honarabul Debo Olagunagba wasu kalaman mai ne kawai na wasan kwaiwakyo da wanda bai san siyasa musamman a Jihar Zamfara da arewacin Najeriya ya aikata. Saboda haka ne aka bashi shawarar cewa kada ya bari ayi amfani da shi har a karkatar da shi kawai domin ya na can a cikin na’urar sanyi a ofishinsa da ke Wadata Filaza a Abuja.
Muna matukar damuwa da cewa mutum mai.matsayi iron nasa zai samu labari irin wannan mara tushe balantana makama a game da Jam’iyyarsa da suka shafi PDP reshen Jihar Zamfara amma kawai sai ya kaiwa kafafen yada labarai. Bayanin da ya raba wa manema labarai har aka yi bayanin cewa musabbabin hakan da kuma dalilinsa.abin da bayanin manema labarai ya kuma hakika mai zubar da mutunci ne domin babu hujjoji ko kadan.
Bayanin da ke cikin takardar da aka rabawa manema labarai inda aka zargi yan Sanda da Gwamnatin Jihar Zamfara daga jam’iyyar PDP ofishinsu na Abuja wani abin mamaki ne mara tushe da asali, kuma wasu bayanai ne da aka fitar domin karkatar da jama’a da kuma haifar da zaman lafiya da kyakkyawar dangantakar da ake da ita a Jihar Zamfara.
Wasu daga cikin tambayoyin da suke bukatar a mayar da martani daga gamayyar kungiyoyin su ne shin wai daga wane bangare ko bagire ne suke yin wannan zargin wanda dan takarar Gwamnansu tuni aka sallame shi wanda wata kotun da take a cikin tarayyar Najeriya?
Me yasa PDP ta yi shuru lokacin da sabon Gwamnan Jihar Osun da aka Rantsar Ademola Adeleke da ya ambaci cewa canza wasu abubuwan da Gwamna Magabacinsa ya aiwatar da aka yi a bisa dokar kasa?
Da irin abin da ke faruwa a Jihar Zamfara, muna aikawa da sako ga irin wadannan yan siyasar da suke gurbatattu, musamman ga wadanda suke makalewa a karkashin wata jam’iyya domin aiwatar da ta’addancin da ke haifar da tashin tashina.
Muna son su yi hakuri su bar Jihar Zamfara haka nan. Domin irin yadda ake haifar da wasu al’amura hakika ya sabawa doka sakamakon rashin adalci.
Duk wanda ya kasance mai martaba da kuma, da ya kasance wanda ya samu horo kwarai dan asalin arewacin Najeriya mai kyakkyawar al’ada daga iyayensa lallai baya goyon bayan aiwatar da bangar siyasa da kuma yin amfani da wasu mutane da yayansu domin kawai haifar da tashin tashina da lalata kayayyakin jama’a domin kawai biyan wata bukata ta son zuciya.
Mu, muna shawartar jami’an tsaro da kada su yi kasa a Gwiwa wajen ganin an samu zaman lafiya a Jihar Zamfara da kuma irin bukatar da ake da ita na ganin an yi maganin masu daukar nauyin tashin hankali da nufin a ci gaba da samun aiwatar da lamarin siyasa cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya Jihar.
A saboda haka muna yin Allah wadai da irin abin da PDP reshen Jihar Zamfara ke aiwatarwa musamman yadda suke karkatar da dhugabanninsu a Abuja da har yanzu ba su nuna tausayawa balantana a samu jaje a kan abin da ke faruwa a Jihar duk da irin abin da ke faruwa na samun kwanciyar hankali da lumana.
Sakamakon hakan muna son shaidawa PDP da wadanda ke daukar nauyin tashin tashina cewa Gwamnatin Jihar Zamfara zs ta ci gaba da marawa Gwamnatin Matawalle baya saboda irin rikon Amanar dukiya Dukiya aiwatar da aiki bisa tanajin doka da kuma aiwatar da aikin tafiyar da Gwamnati tare da kowa da kowa da ke haifar da ci gaban da kowa ke bukatar samu da tsarin ci gaban tattalin arziki cikin gaggawa a Jihar.
Saboda haka duk wani yunkurin mayar da Jihar Zamfara cikin mawuyacin halin da ta shiga a can baya na bangar siyasa, ayyukan yan bindiga da lalata dukiyar Jama’a duk za su fuskanci matsananciyar turjiya kwarai da hanyar yin aiki da shi
Hakika mutanen Jihar Zamfara na murna da irin rawar da Gwamna Matawalle ke aikatawa a kan harkar tsaro domin samun zaman lafiya a yankin baki daya.
Muna mika cikakkiyar godiya da sa albarka a bisa ga irin ayyukan tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar jama’a da Kwamoshinan yan Sandan Jihar Zamfara ke aiwatarwa,jami’an tsaron yan sandan farin kaya na DSS,Jami’an Civil defence da dukkan sauran jami’an taarobisa iron yadda suke sadaukarwa wajen aikinsu na dawo da zaman lafiya da tsaron dukiyar jama’a a Jihar Jihar sauran Jihohi makyabta.

About andiya

Check Also

NTI in Collaboration with UNESCO TRAINS 250 Teachers on HIV Education, Family Life

By; Imrana Abdullahi The Director and Chief Executive of NTI, Prof. Musa Garba Maitafsir said …

Leave a Reply

Your email address will not be published.