Home / News / BA ZA MU CI AMANAR KU BA – DOKTA DIKKO UMAR RADDA

BA ZA MU CI AMANAR KU BA – DOKTA DIKKO UMAR RADDA

DAGA IMRANA ABDULLAHI

….Matasaaaaa, Mataaaa,ina yi wa kowa fatan alkairi

….bukatarka ta biya gaka ga yan jam’iyyar APC na Jihar Katsina masu yi maka fatan alkairi.

An bayyana mutanen Jihar Katsina da cewa masu godiyar Allah ne da ba su da butulci don haka ake godewa kowa da kowa, yau haske yazo an yi walkiya an haska kowa a Jihar Katsina.

“Kowane dan Jihar katsina na iya gane hannun dama da na hagu,kowane dan Jihar katsina na gane haske da duhu domin haske ya bayyana ana iya gane haske da duhu, kowa zai gane  APC ta bayyana an yi aikace aikace, babu sauran yaudara ba sauran cin Amana babu sauran fitina Allah ya kawo, Allah ya kawo haske a Jihar Katsina zai haska.

Dan takarar Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Dokta Dikko Umar Radda ya ce idan Allah ya amince za mu tsare mutuncin ku, dukiyarku da rayuwarku sai inda karfin mu ya kare da ikon Allah, idan Allah ya yarda zamu inganta Noma zamu inganta ilimi zamu inganta harkokin kiwon lafiya a Jihar Katsina.

Kuma “ina marayu da zawarawa da duk marasa galihu a Jihar Katsina zan kawo maku gata idan Allah ya amince mana, babu shakka ko wata tantama za mu yi maku gata a Jihar Katsina”.

Dikko Radda ya ci gaba da cewa “Jama’ar Jihar Katsina muna yi maku alkawalin cewa za mu kare martaba da mutuncin dukiyarku,rayuwarku tare da naku mutuncin, a cikin shika- shikan mulki a wannan zamanin abin da musulunci ya tabbatar mana shi ne a tsare mutuncin mutane, addininsu kuma a tsare dukiyar su ina gaya maku cewa idan Allah ya yarda nasara ta mu ce.in Allah ya yarda za mu samu ingantattar rayuwa kuma babu yaudara sannan kamar yadda muke gaya maku taken mu shi ne ba cuta ba cutarwa ( La Zara wala zarara) ba za mu cuce kuba ba za mu bari a cuce ku ba.

Dikko ya kara da yin hamdala, inda ya ce mai girma Gwamna muna godiya, mai girma shugaban kasa muna godiya kwarai,haka nan matasa muna godiya yan jam’iyyar APC na Jihar Katsina duk muna godiya, mutanen Jihar Katsina muna godiya tare da manyan bakin da suka halarci wannan gagarumin taron gangamin duk muna godiya, Allah ya mayar da kowa gida lafiya.

Alhaji Ahmad Dan Giwa Darakta janar na Yakin neman zaben Gwamnan Jihar Katsina na jam’iyyar APC kara fadakar da jama’a ya yi cewa hakika jam’iyyar APC ta taka rawar gani wajen aiwatar da ayyukan raya kasa a duk fadin Jihar da kasa baki daya.

“Daga yau an bude kamfe na neman zabe a Jihar, za a kuma fara yin Yakin neman zabe a ranar Laraba mai zuwa daga karamar hukuma zuwa karamar hukuma. Za kuma a fara da yankin Daura kuma za a fara ne da karamar hukumar Baure a ranar Laraba sai Alhamis a ta fi karamar hukumar Sandamu sai Zango sai Daura sai mu gangaro had ya zuwa Kusada da Kankiya. Sannan sai a dan huta sai a dauki shiyyar Katsina Sai kuma a ta fi shiyyar Funtuwa a kuma sake dawowa wannan garin mai albarka gari na Faskari”.

Kuma “abin da muke so ga dukkan yayan jam’iyyar APC shi ne a tabbatar da yin kamfe cikin lumana da kwanciyar hankali, saboda kamfe sin da za a yi na fadawa jama’a ne irin abubuwan da APC ta yi wa al’umma ne na alkairi har aka samu gagarumin ci gaban da ake gani a halin yanzu tun daga matakin kasa, kananan hukumomi zuwa Jihohi baki daya, muna tabbatar maku cewa kuma da nasara ba wai a Jihar Katsina kawai ba har a kasa baki daya. Da ikon Allah Sanata Bola Ahmad Tinubu sai ya bar tarihi a Najeriya kamar yadda ya bari a Jihar Legas lokacin da ya zama Gwamnan Jihar Legas, kuma a nan Jihar Katsina ma Dikko Umar Radda shima zai bar tarihi ya Dora daga inda mai girma Gwamna Aminu Bello Masari ya tsaya har ma ya Dora bisa sosai, akwai abubuwan da aka yi na ayyukan ciyar da jama’a gaba na S – Power,Suwapee da kuma ciyar da dalibai na makaranta. Ina tabbatar wa ma’aikatan Jihar Katsina cewa za a Dora daga inda Gwamna Aminu Bello Masari ya ajiye, tun da wannan Gwamnatin ta hau Aminu Bello Masari bai taba tsallake wani watan da ba a biya Albashi ba don haka za a ci gaba da aiwatar da hakan har ma a Dora da dimbin abubuwan alkairi da ikon Allah, ku Sani cewa jam’iyyar APC ta kafa tarihi a Najeriya har ga shugaba Muhammadu Buhari ya gano ainihin mai a arewacin Najeriya wanda hakan martaba ce a Arewa domin ana yi mana gori cewa mun zama cima zaune to, yanzu an gano mai a arewacin Najeriya. Har akwai mai a Gombe da Bauchi za kuma a ci gaba da neman mai a Jihohin Zamfara da Bauchi da sauran Jihohin arewa da aka san akwai Mai a arewacin Najeriya, neman man nan karin martaba, daraja da mutunci ne ga arewacin Najeriya

Da yake tofa albarkacin bakinsa kwamared Isiyaku Wada Faskari,kuma kodineta na dan takarar Gwamnan Jihar Katsina karkashin APC a karamar hukumar Faskari wato Dokta Dikko Umar Radda,”hakika muna yi wa Allah godiya da aka yi taro lafiya kuma aka gama lafiya ba ko tari ko Dambe a tsakanin wani da wani kuma abu na biyu kuma shi ne wannan gangamin da aka yi a karamar hukumar Faskari ya nuna cewa jam’iyyar APC za ta yi nasara da ikon Allah.

A dukkan abubuwan da suka gudana ya nuna cewa jama’a suna nan tare da wannan jam’iyya da ke da Gwamnati domin har yanzu suna da kyakkyawan fata da zato a wannan jam’iyyar.

Taro ne da ya girgiza hankalin wanda ke adawa da wannan jam’iyyar domin wannan taron ya nuna wa masu adawa cewa duk mai kudi kawai a boye abinsa kada ma ya sake ayi masa sakiyar da ba ruwa har ya yi asarar kudinsa.   

About andiya

Check Also

Alleged budget padding : Northern NASS member shun rancour, disunity, to enhance developmental projects 

Kola Kano and Imrana Abdullahi NORTHERN members in the national assembly, have been called upon,not …

Leave a Reply

Your email address will not be published.