Home / News / APC MU HADA KAI DOMIN SAMUN NASARA – ABDULLAHI SHEME

APC MU HADA KAI DOMIN SAMUN NASARA – ABDULLAHI SHEME

IMRANA ABDULLAHI
Wani jogo a jam’iyyar APC daga karamar hukumar Faskari a Jihar Katsina Alhaji Abdullahi Haruna Sheme da ake yi wa lakabi da ” go free” ya yi kira ga daukacin yayan jam’iyyar da su hada kai domin samun nasarar lashe zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Abdullahi Haruna Sheme ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai, inda ya ce batun yin cece – kuce a tsakanin yayan jam’iyya kamar ana gamayya game da batun dan takarar da karamar hukumar Kafur suka zaba a lokacin zaben fitar da dan takara wannan duk ba shi ne abin yi ba saboda tuni aka rigaya aka kammala zaben kuma Allah ya ba dan takarar Gwamnan Jihar Katsina karkashin APC nasara kuma Wanda ya samu nasarar shi ne Dokta Dikko Umar Radda don haka kawai a taru ayi aiki domin samun nasara ta yadda bukata za ta biya nufi kawai shi ne mafita amma ba kace – nace ba.
“Wadanda suka yi zaben fitar da dan takara daga karamar hukumar Kafur sun zabi Masanawa be ba su zabi Dokta Dikko Umar Radda ba ko Dokta Mustapha Muhammad Inuwa don haka meye na maganganu kuma Gwamna Masari ya fitar da kansa domin bai nuna goyon bayan kowa ne dan takara ba kamar yadda ya bayyana.
Abdullahi Haruna ya ci gaba da cewa ” ina yin kira ga daukacin yayan APC a ko’in suke a fadin Jihar da su hada kai a tabbatar da taken jam’iyya na tsintsiya madaurinki daya, kuma ina shaidawa duniya cewa no ban iya siyasar kudi ba don haka ba wanda ya ba ni kudi, siyasar da na iya ita ce ta mutunta jama’a ganin girma da yi wa kowa adalci kawai.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.