Daga Imrana Abdullahi
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana aniyar jam’iyyar na karbar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP idan ya amince ya koma jam’iyya mai mulki.
Dokta Ganduje ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai bayan ya karbi bakuncin tsohon sakataren gwamnatin tarayya Anyim Pius Anyim a gidansa da ke Abuja.
Ya ce, “Ba wanda zai ce Kwankwaso ba dan siyasa ba ne, ko kadan ya yi Gwamna Kano sau biyu, duk da cewa a cikin wa’adin mulkin da aka samu, ya kasance Ministan tsaro, duk da cewa bai san me ake nufi da tsaro ba, kuma ya kasance, ya taba zama Sanata, duk da cewa bai taba cewa komai ba tsawon zamansa a wurin.
“Amma idan har yana so ya koma APC, kofarmu a bude take, musamman a yanzu da wani dan jihar sa ne shugaban jam’iyyar, don haka zai yi masa sauki ya yi ta kai ruwa rana.”
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa aka bar Kwankwaso cikin jerin sunayen ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya nada, Ganduje ya bayyana cewa tun farko ba a yi wa dan takarar NNPP alkawarin komai ba.
Ya fara samun labarin ne daga bakin Kwankwaso da kansa bayan ya dawo daga ganawarsa da shugaban kasar a birnin Paris na kasar Faransa.
“Gaskiya ne Shugaba Tinubu ya yi alkawarin tafiyar da gwamnatin hadin kan kasa, kuma ya tsaya kan kalamansa. Nyesom Wike, daga jam’iyyar PDP, yanzu ya zama daga cikin jerin wadanda majalisar Dattawa ta tantance sunayen su. Amma shi (Kwankwaso) shi ne ya ce tun farko za a ba shi mukami, ba shugaban kasa da kansa ba,” ya kara da cewa.