Home / Big News / APC Za Ta Lashe Zabe A Kebbi Da Kasa Baki Daya – Minista Sununu 

APC Za Ta Lashe Zabe A Kebbi Da Kasa Baki Daya – Minista Sununu 

Daga Imrana Abdullahi
Dokta Yusuf Tanko Sununu, Minista ne a ma’aikatar kula da ayyukan jin kai da ayyukan rage radadin Talauci a Najeriya ya bayyana babban taron shirya na jam’iyyar APC a yankin arewa maso Yamma da cewa lallai abin murna da farin ciki ne da ya kamata kowa ya yi alfahari da shi a kasa baki daya.
Dokta Sununu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a harabar filin taron a dakin taro na dandalin Murtala da ke cikin garin Kaduna.
“Hakika Ba wata tantama jam’iyyar APC a hade take a dunkule al’umma daya don haka ita ce jam’iyyar kasa baki daya kamar dai yadda alamar taken jam’iyyar yake a hadu tare baki daya a dunkule wuri guda don haka ne muke murna da farin ciki a koda yaushe don haka muke ta kokarin ganin mun ci gaba da wannan tafiyar tare da a karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmad Tinubu da Kwamared Nasiru Idris Kauran Abdullahin Gwandu a matakin jihar Kebbi wanda hakan zai bayar da damar ci gaba da ayyukan alkairi a kasa.
Dokta Sununu, ya ci gaba da bayanin cewa babu wata jam’iyya a Jihar Kebbi in ba APC ba domin ita ce abin alfaharin kowa a jihar sakamakon irin ayyukan da take aiwatarwa wajen ci gaban jama’a. Kuma muna sane kamar kowa wata jam’iyyar ma ta ADC na da shugabannin Jiha guda biyu ne daya Kotu ta amince da shi dayan kuma kotun ba ta amince da shi ba Sam, don haka jam’iyyar APC ita ce jam’iyyar daya a dunkule wuri guda tare da hadin kai a tsakanin ya’yan ta.
Kuma, ” mu a jihar Kebbi muna daga cikin jihohin da suke sa’ar samun ribar dimokuraɗiyyar a Najeriya, a Misali akwai ayyukan tituna kamar na titin  Illela Badagiri da aikin Zuru zuwa Dabai da kuma aikin Wara da ya kasance tuni ya na a kasa ga aikin kwalejin kimiyyar Kere- Kere da ke Yawuri da kuma aikin Kwalejin Foli ta Birnin Kebbi duk da nufin a samu matasan mu suje su yi karatu a wadannan makarantu, kowane mutum da ke a jihar Kebbi sako da lungu zai gaya maka hakan irin ci gaban da aka samu karkashin jagorancin Kauran Gwandu mai raya karkara da birane baki daya.

About andiya

Check Also

Dangote Refinery Recalls Redeployed Engineers

    Dangote Petroleum Refinery has approved the recall of engineers previously redeployed across its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.