Home / Big News / Jam’iyyar APC Jirgin Tsira Ce – honarabul Ibrahim Almustapha

Jam’iyyar APC Jirgin Tsira Ce – honarabul Ibrahim Almustapha

 

Daga Imrana Abdullahi
Dan Majalisar Wakilai Ta Tarayya daga Jihar Sakkwato honarabul Ibrahim Al Mustapha Aliyu, ya yi kira ga daukacin jama’a da su kara himma wajen bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jam’iyyar APC a shiyyar arewacin Najeriya da kasar baki daya.

Honarabul Ibrahim Al Mustapha Aliyu, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron shiyyar arewa maso yamma na jam’iyyar APC da ya gudana a Kaduna.
Honarabul Almustapha Aliyu, wanda ke wakilta kananan hukumomin Raba da Wurin a majalisar tarayya ya ce babu sauran wata jam’iyya mai rai da ta wuce APC, don haka kowa ya taho ya rungumi jam’iyyar APC kasancewarta a matsayin Jirgin tsira.
“Idan aka duba sosai da idanun basira za a ga irin muhimman ci gaban raya kasa da ake samu a jihar Sakkwato da kasa baki daya don haka muna kara yin kira ga kowa ya rungumi jam’iyyar APC a matsayin Jirgin tsira”.

About andiya

Check Also

Dangote Refinery Recalls Redeployed Engineers

    Dangote Petroleum Refinery has approved the recall of engineers previously redeployed across its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.