Home / Kasuwanci / Babban Bankin Najeriya Ya Hanzarta Cire Dokar Kwasar Kudi – Gudaji Kazaure

Babban Bankin Najeriya Ya Hanzarta Cire Dokar Kwasar Kudi – Gudaji Kazaure

Mustapha Imrana Abdullahi
An yi kira ga babban Bankin Najeriya da ya hanzarta cire dokar da ya Sanya ta diban kudin masu ajiya a Bankuna ta cirar naira dubu 15,000 a cikin kudin da mai ajiya ya kai Banki da duka kai naira dubu dari biyar.
Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure wanda dan majalisar wakilai ne ta tarayya daga Jihar Jigawa ya yi wannan kiran lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta bbc.
Honarabul Gudaji Kazaure ya ce ta yaya mutum da ya kai kudinsa Banki domin gudun barayi sai kuma a cire masa dubu Goma sha biya a banki don kawai ya kai masu dubu dari biyar, lallai wannan abin dubawa ne tun da wuri.
“Ko wadanda suka gabata da ake ganin sun kwashe dukiyar kasa sun yi gaba da ita ba su kakabawa jama’ar kasa irin wannan ba sai, mu da muka zo yin gyara ga tattalin arzikin kasa sannan a rika Sanya wa jama’a irin wannan dokar, to ina amfanin gudun da mutane kan yi na gudun barayi suke ajiye kudi a cikin gidajensu sai su kai Banki kuma duk da haka an gudu kenan ba a tsira ba”, inji Honarabul Gudaji Kazaure.
“Saboda haka ne muke yin kira ga shugaban babban Bankin Najeriya da ya sake yin tunani game da wannan tsarin na kwashe kudin mutane”.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.